'Kamar Libya, Iraq,' Sowore Ya Fadi Hadarin Zuwan Sojojin Amurka Najeriya
- Omoyele Sowore ya soki barazanar shugaban Amurka Donald Trump ta nuna son turo sojoji su yi yaki a Najeriya
- Ya ce irin wadannan mamaya da Amurka ta yi a kasashen da suka gabata sun kara shiga rikici maimakon zaman lafiya
- Kwamred Sowore ya gargadi ‘yan Najeriya da kada su dogara ga kasashen waje wajen warware matsalolin cikin gida
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da barazanar shugaba Donald Trump ta shigar da sojojin Amurka Najeriya.
Trump ya bayyana cewa yana tunanin tura sojojin Amurka “da bindigogi a hannu” idan gwamnati ta kasa dakatar da kashe Kiristoci da kungiyoyin da ya kira masu tsattsauran ra’ayi ke yi.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa Sowore ya yi martai ga Trump ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sowore ya ce yunkurin na iya jefa Najeriya cikin mummunan hali, yana mai cewa irin wadannan tsoma bakin kasashen waje a baya sun fi haifar da rikici fiye da warware matsaloli.
Gargadin Sowore kan mamayar Amurka
Sowore ya bayyana cewa kalaman Trump na iya burge wasu, amma tarihi ya tabbatar da cewa irin mamayar Amurka ba sa kawo mafita.
Ya ce:
“Barazanar mamayar soja da Trump ya yi don kare Kiristoci a Najeriya na iya zama abin sha’awa ga wasu, amma tarihi ya nuna cewa hakan yana da hadari.”
Ya ambaci misalan Afghanistan, Iraq, Libya da Siriya, inda ya ce mamayar sojojin Amurka ta bar wadannan kasashe cikin halin rashin tsaro da rudani.
“A duk inda Amurka da kawayenta suka mamaye, suna barin kasar cikin halin da ya fi na da,”
Inji Sowore
“Ba mu bukatar ceto daga waje,” Sowore
The Guardian ta rahoto cewa Sowore ya jaddada cewa mafita ga matsalolin Najeriya na cikin gida ne, ba daga kasashen waje ba.

Source: Getty Images
Ya ce abin da ake bukata shi ne shugabanci na gaskiya, wanda zai kare rayuka da dukiyar jama’a tare da tabbatar da adalci.
A cewarsa:
“Abin da Najeriya ke bukata ba wani mai ceton waje ba ne, sai dai shugabanni nagari masu gaskiya da riƙon amana da za su kawo karshen rashawa da zalunci.”
Ya kara da cewa matsalolin Najeriya ba za su taba warwarewa da tayar da bom ko sojojin kasashen waje ba.
Gargadin Sowore ga Kiristoci da Musulmai
Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya ce barazanar Trump tana da tushe ne na siyasa, ba tausayi ba.
A cewarsa:
“Donald Trump bai damu da ‘yan Najeriya ba — ko Kiristoci, ko Musulmai, ko kowa ba. Warware matsalolinmu ba zai taba zuwa daga kasashen waje ba,”

Kara karanta wannan
Yadda ta kaya tsakanin Buhari da Trump a fadar White House kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Martanin gwamnatin Tinubu ga Trump
A wani martani na dabam, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karyata ikirarin Amurka cewa Najeriya na take hakkokin addini.
Ya ce Najeriya kasa ce ta dimokuradiyya da ke tafiyar da mulki bisa kundin tsarin kasa, wadda ke tabbatar da ‘yancin addini ga kowa.
Najeriya dai ta taba shiga jerin kasashen da ake zargi da take hakkin addini a shekarar 2020 karkashin gwamnatin Trump, kafin a cire ta daga jerin a 2021 lokacin mulkin Joe Biden.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

