Sauki Ya Samu: Farashin Shigo da Man Fetur a Najeriya Ya Ragu zuwa Kasa da N830
- Farashin shigo da kowace litar man fetur a Najeriya ya ragu zuwa N829.77, ƙasa da na Dangote da ke sayar da litar a kan N877
- Wannan na zuwa ne yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da harajin shigo da mai na 15% saboda wasu dalilai
- Duk da raguwar farashin shigo da fetur, an ce gidaje mai a Lagos da Ogun sun ki sauke nasu, inda lita ta kai N920 yanzu
- Manajan gidan man Shade da ke Kaduna, Alhaji Mubarak Aliyu, ya yi tsokaci kan sauyin farashin fetur da ake samu a Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Farashin shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya sauka zuwa ₦829.77 a kan kowace lita, bisa rahoton Ƙungiyar Manyan ’Yan Kasuwar Makamashi ta Najeriya (MEMAN).
Rahoton ya nuna cewa wannan sabon farashin ya ragu sosai idan aka kwatanta da na farashin matatar Dangote, wanda ke sayar da litar a kan ₦877.

Source: Getty Images
A cikin makonni da suka gabata, farashin shigo da mai ya ragu daga ₦849.61 a ranar 13 ga Oktoba zuwa ₦839.97 a ranar 21 ga Oktoba in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin litar man fetur a Najeriya
Sai dai duk da haka, farashin litar fetur a gidajen mai a jihohin Lagos da Ogun ya ci gaba da kasancewa ₦920, alamar cewa farashin bai sauka a kasuwa ba tukuna.
Bisa bayanan Petroleumprice.ng, farashin man fetur a rumbunan manyan 'yan kasuwar mai a ranar Lahadi ya kasance kamar haka:
- Dangote – ₦873;
- Pinnacle – ₦872;
- NIPCO – ₦872;
- Matrix – ₦872;
- AA Rano da Aiteo – ₦871;
- Ardova – ₦872;
- Eterna – ₦874;
- Bono da Gulf Treasure – ₦875;
- Prudent – ₦890.
Masana sun bayyana cewa bambancin farashin tsakanin man waje da na cikin gida ya samo asali ne daga haraji, kuɗin sufuri, da sauye-sauyen kasuwa.
Harajin 15% na shigo da man fetur
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da 15% na harajin shigo da fetur da dizal, domin ƙarfafa tace man cikin gida da rage dogaro da shigo da mai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sunday Dare, mai ba shugaban kasa shawara kan hulɗar jama’a da watsa labarai, ya ce manufar karin harajin ita ce gyara tsarin makamashi a ƙasar nan.
“Shekaru da dama Najeriya tana dogaro da mai daga waje duk da kasancewarta mai arzikin man fetur. Wannan mataki zai kare masana’antun cikin gida kuma ya samar da ayyukan yi,” in ji Dare.

Source: Twitter
Mayar da hankali kan tace mai a gida
Sunday Dare ya ce karin harajin zai sanya man da aka shigo da shi daga waje ya zama ba shi da riba sosai, ta yadda man da aka tace a cikin gida, kamar a matatar Dangote, Port Harcourt, da kananan matatun mai zai fi kima.
Masana tattalin arziki sun ce wannan mataki zai taimaka wajen daidaita kasuwar dalar waje, jawo zuba jari a sashen man fetur, da tabbatar da ’yancin makamashi ga ƙasar.
Ko da yake ana iya samun ɗan tashin farashi na wucin gadi, gwamnati ta ce wannan sauyi yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da dogaro da kai da ingantaccen makoma ta tattalin arzikin makamashi.
Farashin fetur a Kaduna
A zantawar Legit Hausa da wani manajan gidan man Shade da ke Kaduna, Alhaji Mubarak Aliyu, ya shaida mana cewa ana samun saukin fetur a yanzu.
Alhaji Mubarak ya ce:
"Idan har matatar man Dangote za ta ci gaba da sauke farashin mai idan an samu saukar shi a duniya, to tabbas litar fetur za ta koma ƙasa da N700.
"Ana ci gaba da samun kasashen da ke hako mai, kasuwar duniya na ganin karuwar danyen mai, sannan kasashe da dama sun koma tace man su, dole farashi ya sauka.
"Mu ma a nan cikin gida, idan matatar man Kaduna, Fatakwal da sauransu suka dawo aiki, za a samu sauki. Yanzu litar mai tana tsakanin N995 har sama da haka a wasu wurare."

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya
Litar fetur ta yi tsada a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar IPMAN ta koka kan tashin farashin litar mai duk da gangar danyen mai ta sauka a kasuwar duniya.
Bincike ya nuna cewa farashin da ake sayar da kowace litar fetur ya kai N955 zuwa N960 a wasu gidajen mai da ke a birnin tarayya Abuja da kewaye.
Sai dai kungiyar dillalan man fetur din suna ganin tsadar da aka samu na da nasaba da rashin ba su damar sayen fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


