Masana’antar Kannywood Ta Yi Babban Rashi, Allah Ya Karbi Ran Malam Nata’ala
- An shiga jimami a masana'antar Kannywood bayan saanr da rasuwar fitaccen dan wasa da ya ba da gudunmawa
- Jarumin Kannywood, Mato Yakubu da aka fi sani da Malam Nata’ala, ya rasu bayan fama da ciwon daji a yau Lahadi 2 ga watan Nuwambar 2025
- Marigayin ya dade yana neman taimako kan rashin lafiya inda Gwamnatin Yobe da shugaban Nijar suka taimaka masa da kuɗi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rahotannin da muke samu yanzu sun tabbatar da rasuwar fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood bayan fama da jinya.
Mun samu labarin rasuwar shahararren jarumin Kannywood, Mato Yakubu, wanda mutane suka fi sani da Malam Nata’ala daga shirin Dadin Kowa.

Source: Facebook
Marubuciya Fauziyya D. Sulaiman ce ta bayyana haka a Facebook a yau Lahadi 2 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan
"Nan gaba za ku gode mini," Gwamma Diri ya fadi asalin dalilin ficewarsa daga PDP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda marigayin ya samu sunan Malam Nata'ala
Marigayin ya yi kaurin suna a fina-finai da dama da aka yi a masana'antar Kannywood inda ya shafe shekaru yana ba da gudunmawa.
Sai dai ya sake sanuwa ne sosai a shirin Dadin Kowa da gidan talabijin na Arewa24 ke gabatarwa mai dogon zango.
A cikin Dadin Kowa ne marigayin ya samu sunan Malam Nata'ala a matsayin malamin allo kuma mai almajirai wanda ya kayatar da shirin sosai.
Taimako daga Gwamna Buni da Tchiani na Nijar
Malam Nata’ala ya dade yana fama da rashin lafiya, inda ya rika neman taimakon jama’a a bidiyo, yana roƙon mutane su taimaka masa don magani.
Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki nauyin kula da lafiyarsa, haka kuma ya bayyana cewa shugaban ƙasar Nijar ya taimaka masa da kuɗi domin ci gaba da jinya.
Kafin Gwamna Mai Mala Buni ya taimaka masa sai da ya yi bidiyo yana zargin ko an hada su da gwamnan duba da alakar da suke da shi a baya.
A wannan bidiyo din ne ya ke fadin irin alherin da ya samu daga shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani da cewa na kusa da shi ba su taimaka masa ba.
Daga bisani, gwamnan ya yanke shawarar daukar nauyin jinyarsa a matsayinsa na dan asalin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Nata'ala ya bar duniya bayan fama da jinya
A karshe, bayan gwagwarmayar da ya yi da rashin lafiya da shan magani, Allah ya yi masa rasuwa, lamarin da ya sa masoyansa da masana’antar Kannywood cikin jimami.
Fauziyya D Sulaiman ta tura sakon ta’aziyya, tana addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma fatan jinya ya zama kaffara.
A cikin rubutunta, Fauziyya ta ce:
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, yanzu na ke samun labarin rasuwar Malam Nata'ala, Allah ya gafarta masa, Allah ya sa jinya ta zama kaffara."
Nata'ala ya nemi taimakon al'umma saboda jinya
A baya, kun ji cewa marigayi jarumin Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata’ala ya bayyana mawuyacin hali da ya shiga.
Malam Nata’ala kafin rasuwarsa ya tabbatar da cewa yana fama da cutar daji, inda ya bayyana bukatar taimakon addu’o’in al'umma da kudi.
Jarumin ya godewa masu taimaka masa ciki har da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malaman addini da masana’antar Kannywood.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

