Ana Tsaka da Jiran Sakamakon Zaɓe, an Bankawa Ofishin INEC Wuta a Niger

Ana Tsaka da Jiran Sakamakon Zaɓe, an Bankawa Ofishin INEC Wuta a Niger

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa masu zanga-zanga sun bankawa ofishin hukumar zabe ta INEC wuta a Niger
  • Masu zanga-zangar a Nasko da ke Magama, sun ƙone ofishin bayan zargin rasa takardun sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi
  • An ce jami'ai sun kawo katin jefa ƙuri’a ba tare da sakamakon ba, lamarin da ya tayar da hankula a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Yayin da ake jiran sakamakon zaben ƙananan hukumomi a Niger, an kona ofishin hukumar zabe ta INEC.

An kona ofishin hukumar ne a Nasko da ke karamar hukumar Magama bayan matasa sun fusata.

An kona ofishin hukumar zabe a Niger
Shugaban hukumar zabe a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Zargin da ake yi wa hukumar INEC

Rahoton Tribune ya ce jama’a suna korafi ne kan batun bacewar takardun sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka kawo yankin.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidu sun ce an kawo takardun jefa ƙuri’a ba tare da takardun sakamako ba, abin da ya sa jama’a zargin an shirya yin magudin zaɓe a yankin.

Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka ƙone ofishin INEC, sai dai ba a tantance girman barnar ba amma an lalata muhimman kayan zaɓe.

A wani taron rarraba kayan zaɓe misalin ƙarfe 6:30 na yamma a Magama, wasu ‘yan daba da makamai sun kai hari, suka jikkata ma’aikata sannan suka ƙone kayan.

Kokarin yan sanda kan lamarin

Rundunar ƴan sanda ta Niger ta tura jami’anta domin hana matasa ƙone ginin gaba ɗaya, tare da cafke wasu daga cikin wadanda ake zargi da laifin.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ga manema labarai a Minna ranar Asabar 1 ga watan Oktoban 2025.

Sanarwar ta ce ana ci gaba da bincike kan mutanen da aka kama da kuma musabbabin tashin hankalin da ya faru a yankin Magama, cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Guinea Bissau bayan yunkurin juyin mulki

Gwamna Bago ya shawarci yan jinarsa kan zabe
Gwamnan jihar Niger, Umaru Bago. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Facebook

Shawarar da Gwamna Bago ya ba al'umma

A gefe guda, Gwamna Umaru Bago ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da shiga tsarin zaɓe, yana cewa dimokuraɗiyya ta daɗe a ƙasar nan.

Ya yi wannan bayanin ne bayan ya kada ƙuri’arsa a rumfar zaɓe ta Tswashagi Raba, Landzun, a yayin zaɓen ƙananan hukumomin jihar Niger.

Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu saboda tilasta gudanar da zaɓe a matakin ƙananan hukumomi, yana cewa fitowar jama’a "abin mamaki ne kuma na tarihi".

Dan takarar APC a Bida, Muhammed Usman-Manko, ya gode wa jama’a saboda fitowarsu sosai, yana cewa goyon bayan jama’a ya nuna irin ayyukan alheri na gwamnati.

An kona ofishin INEC a Benue

Kun ji cewa wasu fusatattun matasa a ranar Laraba 3 ga watan Yulin 2024 sun kai hari wani ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa INEC tare da ƙona shi a jihar Benue.

Kara karanta wannan

Samia Suluhu: Mace ta lashe zaben shugaban kasar Tanzania

Matasan da ke zanga-zangar nuna adawa da hare-haren ƴan bindiga sun ƙona ofishin INEC da ke Sankara, hedkwatar ƙaramar hukumar Ukum.

Kwamishinan INEC a birnin Abuja, Sam Olumekun, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa tare da bayyana abin da ya faru.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.