Amurka Ta Gindayawa Najeriya Sharadi bayan Barazanar Kawo Hari kan Zargin Kisan Kiristoci
- Dan majalisar Amurka Riley M. Moore ya gargadi gwamnatin Najeriya kan zargin kashe-kashen Kiristoci a ƙasar
- Ya ce gwamnatin Amurka ba za ta ƙara yin shiru ba idan ba a ɗauki mataki ba, juma'a shirye kasarsa ta ke ta dauki mataki
- Wasu 'yan Najeriya sun maida martani, suna cewa Amurka ta daina barazanga kasa mai ikon cin gashin kanta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Dan majalisa Riley M. Moore, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da kashe-kashen da suke zargin ana yiwa kiristoci a ƙasar.
A wani gargadi da ya fitar dauke da sakon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce kasarsa ba za ta cigaba da yin shiru a kan lamarin ba.

Kara karanta wannan
Hana shari'ar Musulunci a Najeriya: Bashir Ahmad ya yi martani mai zafi kan sanatan Amurka

Source: Facebook
A wata sanarwa da ya wallafa a X, Moore ya ce Shugaba Donald Trump ya riga ya yi gargaɗi cewa idan Najeriya ta kasa ɗaukar mataki, gwamnatin Amurka za ta yi gaban kanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka ta gargaɗi Tinubu
Bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yiwa Najeriya, dan majalisarsa ya aika sabon sako ga Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa matukar Najeriya ta ki baiwa Amurka hadin kai don magance matsalar, za a dauki matakin da ya dace a kan kasar.
Ya ƙara da cewa burin su shi ne a samu zaman lafiya a Najeriya, musamman ga Kiristocin dake zaune a kasar.

Source: Twitter
Riley M. Moore ya kara jan hankalin gwamnatin Najeriya da ta haɗa kai da Amurka wajen kawo karshen wannan mummunan lamari dake faruwa a kasar.
Ya ce:
"Ba za mu bari ƙofar jahannama ta rinjayi masu imani ba.'
Martann yan jama'a ga gwamnatin Amurka
Jama'a da dama sun yi martani ga wannan gargadi daga Moore da Trump, inda aka samu masu goyon bayan Amurka da masu ganin wannan cin mutuncin yancin Najeriya ne.
@kachi_paul ya ce:
"Idan Amurka na son taimaka wa Najeriya, ya kamata ta yi hakan cikin mutunci, ta hanyar raba bayanan sirri, horar da jami’ai da kuma sanya takunkumi na tattalin arziki ga masu hannu a kashe-kashen — ba wai yin barazana da zai janyo rikici ba."
@tolu225 ya bayyana cewa:
"Amfani da ƙarfin soja ko tsoma baki kai tsaye zai iya haddasa tashin hankali da tauye yancin Najeriya. Takunkumin tattalin arziki da tsauraran matakan diflomasiyya su ne mafita wajen tilasta gwamnatin Najeriya ta kare rayukan ‘yan ƙasa."
@lagcitykeys_ ya ce:
"Irin wannan furuci ake yi wa shugabannin Turai ko Amurka idan jami’an tsaro nkisa ko cin zarafi? Ko da gwamnatinmu tana da matsaloli, har yanzu gwamnatin dimokuraɗiyya ce, kuma tana da ikon da ya kamata a girmama.”
Martanin Tinubu ga Amurka
A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani kai tsaye ga takwaransa na Amurka, Donald Trump, kan zargin cewa Kiristoci a Najeriya suna fuskantar kisan kare dangi.

Kara karanta wannan
Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
A cikin martaninsa, Tinubu ya ce Najeriya ce ƙasa mai mulkin dimokuradiyya wacce kundin tsarin mulkin ta ke tabbatar da ’yancin addini ga kowa, kuma babu wata tsangawam ga Kiristoci.
Ya ƙara da cewa gwamnati na gudanar da tattaunawa da shugabannin Kiristoci da Musulmai domin samar da zaman lafiya ba tare da la’akari da addini ko yankin da mutum ya fito na.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
