Yadda Tinubu Ya Dora Alhakin Kisan Kiristoci a Najeriya kan Jonathan a 2014
- Zargin yi wa al'ummar Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya na ci gaba da jawo cece-kuce a muhawara mai zafi a sassa daban-daban
- Wannan ya kara kamari ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya cikin kasashe masu matsala ta musamman kan batun cin zarafin Kiristoci
- A shekarar 2014, Shugaba Bola Tinubu ya taba sukar Goodluck Jonathan bayan an farmaki wasu al'ummomin Kiristoci a Arewacin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taba sukar gwamnatin Goodluck Jonathan, kan gazawa wajen kare Kiristoci.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Source: Twitter
Shugaba Bola Tinubu wanda yanzu yake mulki ya yi rubutun ne a wancan lokacin a shafinsa na X da ake kira da Twitter lokacin.

Kara karanta wannan
'Tinubu zai rika karbar harajin shakar iska a Najeriya,' 'Dan takarar Shugaban Kasa a SDP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya taba sukar Jonathan
A watan Janairun 2014, Tinubu, wanda a lokacin yake jagora cikin 'yan adawa, ya zargi Jonathan kan hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Adamawa da suka kai hari kan al’ummomin Kirista.
"Kisan masu ibadar Kirista abin Allah wadai ne kwarai da gaske. Hakan ya sanya ayar tambaya kan kwarewar Jonathan wajen kare rayukan ‘yan Najeriya."
- Goodluck Jonathan
A watan Afrilun 2014, yayin da tashin hankali ya karu, ciki har da fashewar bam a Nyanya, Abuja, Tinubu ya sake jaddada cewa wajibi ne gwamnati ta tabbatar da tsaron jama’a.
“Zuciyata ta kadu saboda mutuwar ‘yan kasa a Nyanya. Ya kamata a tambayi gwamnatin da ta kasa kare ‘yan kasarta."
- Goodluck Jonathan
An tono kalaman Tinubu kan rashin tsaro
Shekara 11 bayan haka, an tono kalamansa yayin da ake zargin cewa Kiristoci suna fuskantar tashin hankali a sassa da dama na Arewaci da tsakiyar Najeriya.
Jaridar TheCable ta ce rahoton da kungiyar International Society for Civil Liberties and the Rule of Law ta wallafa kwanan nan ya bayyana cewa Kiristoci 7,087 aka kashe cikin kwanaki 220 na shekarar 2025, wanda hakan ke nuna an kashe akalla mutum 32 a rana.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata zargin cewa ana kai harin ne saboda addini, tana mai cewa tashin hankalin da ke da alaka da rikice-rikicen tsaro shafar dukkanin mabiya addinai ne.
Lamarin ya sake jawo hankalin duniya a ranar 31 ga Oktoba, 2025, lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Najeriya a matsayin “kasa mai matsala ta musamman” saboda “barazana ga rayuwar Kiristanci”
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike.
Gwamnatin Tinubu ta yi wa Trump martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta yi wa Donald Trump martani kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya bayyana cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Hakazalika, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Amurka domin karfafa fahimtar juna da haɗin kai a fannin tsaro da zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
