Najeriya Ta Yi wa Trump Martani Mai Zafi kan Zargin Kashe Kiristoci, Ta Ce Karya ne
- Gwamnatin Tarayya ta ce ikirarin Donald Trump na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ba gaskiya ba ne
- Ma'aikatar harkokin waje ta bayyana cewa ’yan Najeriya na rayuwa tare cikin zaman lafiya ba tare da bambancin addini ba
- Gwamnatin Najeriya kara da cewa za ta ci gaba da hulɗa da kasar Amurka domin inganta fahimtar juna da zaman lafiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya bayyana cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan Trump ya fitar da sanarwa a ranar Juma’a yana umartan majalisar Amurka ta yi bincike.

Source: Getty Images
Najeriya ta yi martani ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a shafin ma'aikatar yada labarai na X.

Kara karanta wannan
Trump ya sa Najeriya a jan layi kan zargin kashe Kiristoci, Amurka za ta yi bincike
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin gwamnatin Najeriya ga Trump
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa zargin da Trump ya yi bai dace da halin da ƙasar ke ciki ba kwata-kwata.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnatin tarayya ta lura da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan batun kisan Kiristoci a Najeriya. Wannan ikirari bai nuna gaskiyar yanayin da ake ciki a ƙasar ba.”
Business Day ta rahoto ma’aikatar ta ce ’yan Najeriya masu bin addinai daban-daban sun daɗe suna rayuwa, aiki, da ibada tare cikin zaman lafiya.
Haka kuma ta bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu, Najeriya ta jajirce wajen yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zumuncin addinai, da kare rayuka da haƙƙin dukkan ’yan ƙasa.
Sanarwar ta ce gwamnatin za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Amurka domin ƙarfafa fahimtar juna da haɗin kai a fannin tsaro da zaman lafiya.

Source: Twitter
Zargin da Trump ya yi a Najeriya
A cikin saƙon da ya fitar, Trump ya bayyana cewa Kiristoci na fuskantar “barazanar rayuwa” a Najeriya.

Kara karanta wannan
Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Ya ce:
“ Ana kashe dubban Kiristoci, ’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi ne ke da alhakin wannan kisan."
Maganar da ministan Tinubu ya yi
Kafin maganar Trump, Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi ba gaskiya ba ne.
A cewarsa:
“Wasu daga cikin bayanan da jami’an Amurka ke amfani da su ba su da tushe. Wadannan miyagun ba sa kai hari ga mabiya addini guda, suna kai wa Musulmi da Kiristoci duka hari, musamman a Arewacin ƙasar.”
Ya jaddada cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da kare dukkan ’yan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
NSCIA ta karyata zargin kashe Kiristoci
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar kolin addinin Musulunci ta karyata zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi.
Rahotanni sun nuna cewa majalisar NSCIA ta yi martani ne yayin da zargin ke kara karbuwa a fadin duniya.
NSCIA ta ce wadanda aka fi kashewa a Najeriya Musulmai ne kuma 'yan ta'adda suna kashe mutane ba tare da lura da addininsu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
