'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki a Kebbi

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki a Kebbi

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kebbi bayan sun kai wani harin da ya ritsa da babban jami'in gwamnati
  • Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi da suka kai hari a garinsa
  • 'Yan bindigan sun sace mataimakin shugaban majalisar ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida da ya kammala sallah a masallaci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun sace mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Hon. Samaila Bagudu.

Miyagun 'yan bindigan sun sace mataimakin shugaban majalisar ne a garinsa na Bagudu da ke cikin karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi.

'Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Rahoton tashar Channels tv ya bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne a garin Bagudu da yammacin Jumma’a, 31 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Ana tuhumar matashi da hallaka mahaifinsa kan hana shi kara mata

'Yan bindiga sun kai hari a Kebbi

'Yan bindigan sun rika harbe-harbe babu kakkautawa domin tsoratar da jama’a a yayin harin da suka kai.

A cewar majiya daga yankin, an sace mataimakin shugaban majalisar dokokin ne jim kadan bayan ya kammala sallah, kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida daga masallaci.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa gwamnati tana bin diddigin al’amarin, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Sai dai, bai yi wani cikakken bayani ba kan yadda lamarin ya auku.

Hakazalika, ba a samu jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ba kan aukuwar lamarin.

Kokarin samun karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.

'Yan bindiga sun kai hari a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun shiga firgici bayan harin, yayin da jami’an tsaro ke cigaba da neman hanyoyin kubutar da mataimakin kakakin tare da tsaurara tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

'Tinubu zai rika karbar harajin shakar iska a Najeriya,' 'Dan takarar Shugaban Kasa a SDP

Harin dai ya nuna yadda 'yan biindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka duk da kokarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi wajen samar da tsaro.

Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin yankin Arewa maso Yamma masu fama da matsalar raahin tsaro wadda 'yan bindiga da 'yan ta'adda suka haifar.

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara yayin wani artabu da suka yi da 'yan bindiga a jihar Kebbi.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga fiye da 80 bayan sun yi yunkurin shigowa jihar Kebbi daga Zamfara.

Hakazalika, sojojin sun yi nasarar kwato babura da dama tare da ceto wasu daga cikin mutanen da 'yan bindigan suka sace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng