‘Azabar Allah na Jiran Ku’: Malamin Musulunci ga Masu Saida Kuri'a a Zabe

‘Azabar Allah na Jiran Ku’: Malamin Musulunci ga Masu Saida Kuri'a a Zabe

  • Malamin Musulunci a Najeriya ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe inda ya gargadi yan kasar da su guji sayar da kuri’a
  • Sheikh Jamiu Amiolohun ya ce karɓar kuɗin siyasa matsala ne kuma za su fuskanci fushin Allah Madaukakin Sarki kan haka
  • Malamin ya bukaci Musulmai su shiga siyasa da gaskiya, su daina zama masu kallo, tare da tsayawa kan adalci da gaskiya a 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Wani malamin addinin Musulunci ya ja kunnen masu kada kuri'a a Najeriya kan illolin sayar da 'yancinsu a zabe.

Malamin daga Ilorin a jihar Kwara Sheikh Jamiu Sanusi Amiolohun, ya gargadi ‘yan Najeriya musamman Musulmai da su guji sayar da kuri’u ko karɓar kuɗi daga ‘yan siyasa.

Malamin Musulunci ya gargadi Musulmai kan sayar da kuri'a
Sheikh Jamiu Amiolohun yayin huduba da Musulmai. Hoto: Anadolu / Contributor, X/@OfficialABAT, TikTok/@Rasaki_olowe_omo_amioloh.
Source: Getty Images

Malamin ya bayyana haka a ranar Juma'a 24 ga watan Oktobar 2025 yayin hudubarsa da aka yada a shafin TikTok.

Kara karanta wannan

Kano: Ana tuhumar matashi da hallaka mahaifinsa kan hana shi kara mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya gargadi masu sayar da kuri'a

Sheikh Jamiu ya ce sayar da kuri'a babban laifi ne yana mai cewa irin wannan aiki yana jawo fushin Allah.

Ya ce Musulmai ba za su zauna a gefe suna kallon siyasa ba, ya kamata su shiga harkar mulki da gwamnati da gaskiya da tsoron Allah.

Malamin ya yi Allah-wadai da masu karɓar kuɗin siyasa domin sayar da kuri’unsu, yana cewa mutanen da ke sayar da yancinsu a lokacin zabe ba su da ikon kuka game da halin da kasa take ciki.

A kalamansa masu tsauri, ya ce:

“Duk wanda ya karɓi kuɗi domin sayar da kuri’a a shekarar 2027 zai fuskanci fushin Allah. Manya da yara, dalibai da kowa, suna sayar da kuri’a sannan suna kuka cewa kasa ta lalace.”
An gargadi Musulmi su guji sayar da kuri'unsu a zabe
Jami'an zabe yayin da ake shirin gudanar da zabe a Najeriya. Hoto: Anadolu/Contributor.
Source: Getty Images

Malamin Musuluncin ya ce Musulmi su shiga siyasa

Sheikh Jamiu ya ce rashin shiga siyasa yana jawo matsaloli ga al’umma, sannan ya jaddada cewa sauyi baya zuwa ta hanyar juyin mulki ko zanga-zanga, sai ta hanyar zabe da bin ka’ida.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Ya kuma gargadi al’umma da su goyi bayan nagartattun ‘yan takara, amma su guji karɓar kuɗin kamfen ko wata kyauta daga ‘yan siyasa.

Malamin ya ce lokaci ya yi da za a tsaya kan gaskiya da adalci domin manufofin al’umma.

A cewarsa:

“Ku Musulman Najeriya, ku shiga siyasa. Ka da ku shiga don sata. Ku fara daga mazabu, ku tsaya takarar kansila, sannan ku nemi shugabancin karamar hukuma. Muna kuka da lalacewar ƙasa, amma mun ki shiga siyasa.”

An gargadi malami kan taba kimar Annabi

Mun ba ku labarin cewa kungiyar Malaman Musulmi na Yarbawa ta gargadi Sheikh Habeeb Adam Al-Ilory kan kalamansa da ake zargin sun saba wa Sahabbai.

Shugaban kungiyar Dr Khidr Mustafa ya ce irin wadannan maganganu na iya kai mutum ga sabawa akida.

Kungiyar ta bukaci Al-Ilory ya dauki hanyar mahaifinsa marigayi Sheikh Adam Al-Ilory wanda ya yi fice wajen hadin kai da hidima.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.