Nuhu Ribadu da Birtaniya Sun Yi Alhini da Kwamishinan Tsaro Ya Rasu a Hadarin Mota

Nuhu Ribadu da Birtaniya Sun Yi Alhini da Kwamishinan Tsaro Ya Rasu a Hadarin Mota

  • Ana ci gaba da tura sakonnin ta'aziyya bisa rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya)
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu da ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya sun yi alhinin wannan rashi
  • Kwamishinan ya rasu ne a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi ranar Juma'a da ta gabata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Mai ba da Shawara Kan Tsaron Kasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya yi ta’aziyyar rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Gumi ya goyi bayan yiwa Maryam Sanda afuwa, ya ce ba a saba dokar Musulunci ba

Nuhu Ribadu ya aika sakon ta'aziyya ga Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da gwamnatin jihar bisa wannan rashi na mutumin kirki da suka yi.

Malam Nuhu Ribadu.
Hoton Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaron Kasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Kanal Bello ya rasu tare da direbansa da dan sandan da ke gadinsa a wani mummunan hadarin mota da ya afku a ranar Juma’a da ta gabata, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nuhu Ribadu ya aika sakon ta'aziyya

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar yau Juma'a, ya ce sakon ta'aziyyar NSA ya isa ga Gwamna Inuwa.

Ya ce Nuhu Ribadu ya aiko sakon ta hannun Dr. Agrih Dauda Sukukum, mataimakin darakta a sashen yaki sa tsattsauran ra’ayi (PCVE) na Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC).

Malam Ribadu ya bayyana marigayi Kanal Bello a matsayin jami’i mai ladabi, gogagge a fannin aiki, kuma dan kishin kasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Najeriya.

A cewar Ribadu:

“Marigayi Kwamishina mutum ne nagari, mai zurfin ilimi kan harkokin tsaro, kuma abokin aikin da ba za a maye gurbinsa ba a sashenmu na yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi matsalar sulhu da 'yan bindiga, ya yi gargadi

"Ya kasance yana bada shawarwari, musamman a Gombe wajen tabbatar da zaman lafiya da canza tunanin tubabbun ‘yan ta’adda.”

Birtaniya ta bi sahun masu alhini

Haka kuma, Ofishin Jakadancin Burtaniya a Najeriya ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin da jama’ar Gombe bisa wannan rashi mai girma, in ji rahoton Punch.

Sakon, wanda Dr. Okoha Ukiwo, jagoran shirin zaman lafiya na SPRiNG ya isar, ya ce marigayi Kanal Bello ya taka rawa wajen karfafa zaman lafiya da hadin kai a Arewa maso Gabas.

Gwamna Inuwa Yahaya.
Hoton Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya a gidan gwamnatin jihar Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Source: Twitter

Gwamna Inuwa ya mika sakon godiya

Da yake godiya, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana marigayi Bello a matsayin jarumin soja, mai amana da nagarta wanda ya bayar da gudunmawa ga ci gaban Gombe da kasa baki ɗaya.

Gwamnan ya gode wa NSA da Ofishin Jakadancin Birtaniya bisa nuna alhini da goyon baya, tare da tabbatar da cewa jihar Gombe za ta ci gaba da ayyukan alherin marigayin.

DPO ta rasu bayan mata aiki a Legas

A wani labarin, kun ji cewa DPO ta yan sandan caji ofis na Festac , CSP Matilda Ngbaronye ta riga mu gidan gaskiya bayan an mata aiki a jihar Legas.

Kara karanta wannan

"Borno ta APC ce," Gwamna Zulum ya tuna alherin da Buhari da Tinubu suka kawo a Arewa

CSP Ngbaronye ta rasu ne ranar 24 ga Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na dare a asibitin Mayriamville Medical Centre da ke Surulere.

Kwamishinan yan sandan Legas, CP Olohondare Jimoh, tare da dukkan jami’ai da ma’aikata, sun mika ta’aziyyarsu ga iyalinta da mahaifiyarta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262