‘Yadda Sabon Tsarin Harajin Tinubu Zai Taimaki Matasa da Kananan ’Yan Kasuwa’
- Gwamnatin Bola Tinubu ta kaddamar da sabon tsarin haraji da zai fara aiki ranar 1 ga Janairun shekarar 2026
- Hadimin shugaban kasan ya ce harajin zai rage wa matasa da kananan ‘yan kasuwa nauyi wajen biyan haraji
- Tope Fasua ya bayyana cewa gwamnati za ta maida hankali kan masu samun kuɗi da yawa, yayin da aka tausayawa marasa karfi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki, Dr. Tope Fasua ya yi magana kan sabon tsarin haraji na Bola Tinubu.
Fasua ya bayyana cewa an tsara sabon tsarin haraji na Najeriya ne domin rage nauyin haraji ga mafi yawan 'yan ƙasa, musamman matasa da kananan ‘yan kasuwa.

Source: Facebook
Yadda yan matasa za su samu sauki
A cewar rahoton Tribune, wannan sabon tsarin haraji da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasua ya yi wannan bayani ne a wani taro mai taken “Sabon Tsarin Haraji na Najeriya: Abubuwan da Matasan Ya Kamata Su Sani” a Abuja.
Ya ce babban burin tsarin shi ne cire wa masu ƙaramin karfi biyan haraji da kuma samar da kudin shiga daga masu karfi a bangaren tattalin arziki.
Ya kara da cewa dokar ta ware masu samun ƙasa da N1m a shekara daga haraji, wato kusan N83,000 a wata gaba ɗaya.
“Yawancin matasa, Shugaban Ƙasa ba ya son ku biya haraji. Wannan shi ne dalilin sabon tsarin haraji.
“Idan kana samun ƙasa da miliyan ɗaya a shekara, ba za ka biya haraji ba. Sai idan ka wuce wannan ne zaka fara biyan kaɗan.”
- Tope Fasua

Source: Twitter
Haraji: Kananan yan kasuwa za su caba
Haka kuma, ya bayyana cewa kananan yan kasuwa da suke juya kuɗi kamar N50m ko ƙasa za a cire su daga biyan haraji, har da VAT.

Kara karanta wannan
'Tinubu zai rika karbar harajin shakar iska a Najeriya,' 'Dan takarar Shugaban Kasa a SDP
Ya ce gwamnati yanzu za ta mai da hankali kan masu kuɗi sosai, musamman a bangaren kasuwar bayan-fage.
Ya kara da cewa:
“Gwamnati tana son tara haraji ne daga riba, ba daga dukkan kuɗin shiga ba, ga masu samun sama da N50m, haraji zai tashi zuwa kusan 24% daga kusan 18%.”
Fasua ya ce manufar sabon tsari shi ne samar da tattalin arziki mai dogaro da kirkire-kirkire, ba kawai saye da sayarwa da dogaro da kaya daga ƙasashen waje ba.
Game da irin sauye-sauyen tattalin arziki da Tinubu ya dauka, ya ce alamun ci gaba sun fara fitowa, duk da tsananin matakan farko.
Yadda farashin mai zai kasance bayan harajin 15%
Kun ji cewa ana sa ran litar man fetur na iya haura N1,000 a gidajen mai bayan gwamnatin Bola Tinubu ta kakaba harajin 15% wajen shigo da mai.
‘Yan kasuwa da masana sun ce matakin zai ƙara tsananin rayuwa ga talakawa a lokacin da tattalin arziki ke fuskantar barazana.
Gwamnatin ta ce manufar ita ce kare masana’antun tace man cikin gida kamar matatar Dangote da sababbin da za a yi wanda ake ta yin korafi a kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
