Dangote Ya Fito Karara Ya Fadi Dalilin Kin Sayen Matatun Man Najeriya
- Alhaji Aliko Dangote ya ce ba zai saye matatun NNPCL ba duk da cewa zai faɗaɗa matatarsa zuwa mafi girma a duniya
- Ya ce kungiyoyi kamar DAPPMAN da sauran attajirai ne ya dace su saye matatun ko kuma su gina nasu da kansu
- Dangote ya ce shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin tallafa wa bangaren fetur da iskar gas da wadataccen danyen mai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba shi da niyyar sayen matatun man fetur na kamfanin NNPCL.
Ya ce ba zai saye su ba duk da cewa zai fadada matatarsa daga tace ganga 650,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a rana.

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana haka ne yayin sanar da fadada matatarsa mai darajar Dala biliyan 20 da ke Legas kamar yadda Radio Now ya wallafa a Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ba zai saye matatun NNPCL ba
Dangote ya ce matatar sa za ta zama mafi girma a duniya, wanda hakan ne ya haifar da tambaya kan dalilin da yasa bai zabi sayen matatun gwamnati ba.
Attajirin wanda ya bayyana hakan tare da abokinsa Femi Otedola, ya ce ya fi son fadada tasa matatar domin gujewa zargin cewa ya cika hadama ko mamaya.
Dangote ya kalubanci DAPPMAN
Dangote ya ce akwai kungiyoyi da mutane masu arziki kamar DAPPMAN da suke da isasshen kudi don sayen matatun NNPCL ko kuma su kafa sababbin matatu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen rage rade-radin cewa shi kadai ke da karfi a kasuwar man fetur a Najeriya.

Source: Twitter
A cewarsa:
“Sayen waɗancan matatun? Da zarar muka taba su, za ku ji hayaniya. Akwai wasu mutane masu kudi sosai, fiye da mu ma, su ne ya kamata su gwada sa’arsu.

Kara karanta wannan
Abin da ya sa litar fetur ta yi tsada a Najeriya duk da gangar mai ta sauka a kasuwar duniya
Akwai kungiyar DAPPMAN — su ne ya dace su saye matatun. Idan ba a sayar da su ba, to su gina nasu.”
Dangote ya kara da cewa idan wasu attajirai suka shiga fannin tace mai, za su kara wa gwamnati karfi wajen cimma manufar raya tattalin arzikin Najeriya.
Dangote ya yaba wa Bola Tinubu
Dangote ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar masa da cewa gwamnati za ta tallafa wajen samar da isasshen danyen mai ga masu tace mai a cikin gida.
Punch ta rahoto ya ce:
“Shugaban kasa na goyon bayan wannan yunkurin tace danyen man mu a gida.
"Mu kuwa muna da dukkanin kayan aiki, shi yasa muka yanke shawarar fadada aikinmu. Mun tsara hakan tun farko,”
Ya ce akwai wasu kamfanoni da suka nuna sha’awar yin hadin gwiwa da NNPCL wajen farfado da tsofaffin matatun Najeriya.
Tinubu ya kawo harajin shigo da mai
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya harajin kashi 15 kan shigo da man fetur.

Kara karanta wannan
Mutanen birnin tarayya za su zauna a duhu, TCN ya fadi dalilin dauke wuta a Abuja
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta sanya harajin ne ba domin kara hanyoyin samun kudi ba, sai dai don karfafa tace mai a cikin gida.
Ana fargabar harajin na iya jawo tashin kudin man fetur a Najeriya, wanda zai iya kara jefa jama'a a matsin tattalin arziki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
