Bayan Tinubu Ya Naɗa Sababbin Hafsoshin Tsaro, An Canjawa Janar Sama da 60 Wurin Aiki

Bayan Tinubu Ya Naɗa Sababbin Hafsoshin Tsaro, An Canjawa Janar Sama da 60 Wurin Aiki

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi sauye-sauye, inda janar-janar 67 suka samu sababbin mukamai da wuraren aiki
  • Wannan na zuwa bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci sababbin hafsoshin tsaron ƙasa da su kawo sakamako a kan rashin tsaro
  • Sababbin manyan hafsoshin soji sun yi alkawarin tabbatar da tsaro ta hanyar dabaru na leken asiri da haɗin gwiwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da rarraba da nada sababbin manyan hafsoshi zuwa muhimman wurare a rundunar domin ƙarfafa jagoranci da inganta tsari.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar-Kolonel Appolonia Anele, da ta bayyana haka ta ce matakin yana nufin sabunta dabarun aiki da kuma ƙara kuzarin rundunar.

Kara karanta wannan

Shirin juyin mulki: Sojoji sun bi diddigin N45bn zuwa hukumar raya Neja Delta

An canjawa sojoji wajen aiki
Shugaba Bola Tinubu tare da sababbin hafsoshin tsaro Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a cikin sababbin nade-naden akwai Manjo Janar Bamidele Alabi, wanda aka nada a matsayin Shugaban Sashen Tsare-tsare da Shirye-shirye na rundunar sojin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojoji ya yi sauye-sauye

Premium Times ta wallafa cewa Manjo Janar Jamal Abdulsalam ya koma Hedikwatar Tsaron ƙasa a matsayin Shugaban Ayyuka; sai kuma Manjo Janar Peter Mala da aka tura zuwa TRADOC a matsayin Kwamanda.

Haka nan Manjo Janar Samson Jiya daga Cibiyar NAHFC ya koma Sashen Kudi da Kasafin Tsaro.

Yayin da wasu kamar Manjo Janar Isa Abdullahi, Musa Etsu-Ndagi, da Mayirenso Saraso suka samu sababbin mukamai a hedikwatar rundunar.

Shugaba Tinubu ya gargadi sojoji

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga sababbin hafsoshin tsaro da su ƙara zage damtse wajen yaƙar ta’addanci, ‘yan fashi, da sauran laifuka a ƙasar.

A wajen bikin nada su a Aso Villa, Tinubu ya ce 'yan Najeriya na bukatar sakamako wajen magance rashin tsaro ba uzuri ba.

Kara karanta wannan

Sababbin hafsoshin tsaro sun san matsayarsu bayan tantance su a majalisa

Ya ce:

"Kada mu bar matsalolin da suka fara tun 2009 su ci gaba.”
Shugaba Tinubu ya gargadi sojoji
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta tallafa masu da kayan aiki da fasahar zamani domin tabbatar da tsaron Najeriya.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da gwamnoni da dama.

Sabon Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya ce za su mai da hankali kan dabarun leken asiri, haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kula da walwalar jami’an soji.

Juyin mulki: Fadar Shugaban kasa ta yi gargadi

A wani labarin, mun wallafa cewa Fadar shugaban ƙasa ta bayyana damuwar ta game da yadda ake yada jita-jita na cewa ana shirin juyin mulki a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce yayin da gwamnati ke ƙoƙarin jawo hankalin masu saka jari zuwa ƙasar, irin wannan labari yana kawo cikas.

Onanuga ya yi kira ga ‘yan jarida da jama’a da su jira sakamakon bincike kafin su fitar da labarai masu sosa zuciya, ya kuma jaddada cewa a daina yada labaran juyin mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng