Yadda Farashin Fetur zai Kasance bayan Tinubu Ya Amince da Harajin 15% a Najeriya
- Litar man fetur na iya haura N1,000 a gidajen mai bayan gwamnatin tarayya ta sanya sabon haraji na 15% wajen shigo da mai
- ‘Yan kasuwa da masana sun ce matakin zai ƙara tsananta rayuwa ga talakawa a lokacin da tattalin arziki ke tangal-tangal
- Gwamnati tarayya ta ce manufar ita ce kare masana’antun tace-man cikin gida kamar matatar Dangote da sababbin da za a yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Farashin man fetur na iya wuce N1,000 a kowace lita bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu da sabon harajin shigo da mai na kashi 15.
Harajin wani ɓangare ne na tsarin gwamnati na kare sababbin masana’antun tace-mai da rage shigo da mai daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan
'Tinubu zai rika karbar harajin shakar iska a Najeriya,' 'Dan takarar Shugaban Kasa a SDP

Source: Getty Images
Yayin hira da Punch, ‘yan kasuwa sun yi gargadin cewa dokar za ta iya haifar da tashin farashi wanda zai ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin halin ƙunci.
Yadda farashin mai zai kasance a Najeriya
Wasu manyan dillalan man fetur sun bayyana damuwa cewa sabon harajin zai ƙara nauyi a kan jama’a.
Wani dilan mai ya ce:
“Farashin man zai iya kaiwa ko wuce N1,000 a lita. Ban ga dalilin ƙara wa mutane wahala ba.”
Wani dan kasuwar ya ce dole ne a jira a ga yadda kasuwa za ta karɓi sabon tsarin kafin a yanke matsaya kan tashin farashi.
Rahoto daga Channels TV ya nuna cewa harajin zai fara aiki ne bayan kwanaki 30, wato daga 21, Nuwamba, 2025, bayan kammala lokacin sauyi da gwamnati ta kayyade.
Ra’ayin IPMAN kan harajin 15% a kan mai
Mataimakin shugaban kungiyar masu sayar da mai ta kasa (IPMAN), Alhaji Hammed Fashola, ya bayyana cewa harajin yana da fa’idodi da illoli.

Kara karanta wannan
Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Ya ce:
“Wannan haraji zai iya hana shigo da mai daga waje, amma zai iya jawo tashin farashi idan ba a kula ba.”
Fashola ya bayyana damuwa cewa tsarin na iya haifar fifiko ga wasu kamfanoni kamar matatar Dangote, idan ba a samar da yanayi mai kyau ba.
Ya kuma gargadi cewa rashin isasshen mai daga matatun cikin gida na iya haifar da karancin mai a ƙasar.
Bukatar gyaran matatun gida Najeriya
Fashola ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da kamfanin NNPCL da su tabbatar da farfaɗo da tsofaffin matatun man Najeriya da ke Fatakwal, Warri da Kaduna.

Source: Twitter
Ya ce:
“Idan matatun cikin gida suka fara aiki yadda ya kamata, to matsalar tsadar man fetur za ta ragu sosai.”
Ya kuma ƙara da cewa, idan sauran matatun masu zaman kansu kamar BUA da sababbin kamfanoni suka fara aiki, za su taimaka wajen rage farashi.
Dalilin Tinubu na saka harajin 15%
A baya mun rahoto muku cewa gwamnatin tarayya ta ce manufar harajin ita ce kare sababbin matatun cikin gida da tabbatar da daidaiton kasuwar man ƙasa.
Umarni kan saka harajin shigo da mai ya fito ne daga wasikar da aka aika ga hukumar haraji ta kasa (FIRS) da hukumar NMDPRA a ranar 21, Oktoba, 2025.
Duk da fargabar karuwar kudin mai a Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko za a samu karin kudi, ba zai wuce N100 a kowace lita ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
