Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Gargadi kan Yada Labaran Yi wa Tinubu Juyin Mulki
- Fadar shugaban kasa ta yi gargadin cewa jita-jitar juyin mulki da ke yawo a kafafen yada labarai na jefa tattalin arzikin ƙasar cikin hadari
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce rahotanni marasa tushe na rage kwarin gwiwar masu zuba jari
- Hadimin shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan jarida su guji yada rade-radi kafin hukumomi su kammala bincike kan zarge zarge
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Fadar shugaban kasa ta bayyana damuwa kan yadda rahotanni marasa tushe na zargin juyin mulki ka iya cutar da tattalin arzikin Najeriya da hana masu zuba jari zuwa ƙasar.
Mai magana da yawun shugaba Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka a daren Alhamis.

Source: Facebook
Yayin wata tattaunawa da tashar Arise News, ya ce yayin da gwamnati ke neman masu zuba jari, irin wadannan jita-jita na iya bata sunan ƙasar da kawo tsaiko ga cigaban tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Illar yada labaran zargin juyin mulki
Bayo Onanuga ya jaddada cewa wajibi ne ‘yan jarida da jama’a su jira sakamakon bincike kafin su fitar da labarai masu sosa zuciya.
A cewarsa, dakarun soji sun tabbatar da cewa akwai bincike da ake gudanarwa kan wasu da aka kama, amma babu wata shaida da ta nuna cewa akwai shirin kifar da gwamnati.
Punch ta wallaa cewa ya ce:
“Lokacin da ƙasa ke neman masu zuba jari, sai ka ga wasu kafafen labarai na ta ihu da cewa an shirya juyin mulki.
"Irin wannan magana tana tsoratar da masu zuba jari. Dole mu jira gaskiya, ba jita-jita ba.”
Suka kan buga labarun juyin mulki a Najeriya
Onanuga ya yi suka kan abin da ya kira son daukar hankali da neman gamsar da masu karatu a yanar gizo, yana mai cewa ba duk wani labari ne ya dace a yada ba.

Kara karanta wannan
Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Source: Twitter
Ya ce wasu kafafen labarai sun buga labarin juyin mulkin ne don jan hankali, ba tare da tabbatar da gaskiyarsa ba, lamarin da ke iya jefa ƙasar cikin rudani.
“Ba wai saboda mutane ba su yarda da gwamnati ba ne sai mu rika yada jita-jita. Akwai alhakin yada gaskiya da ya rataya a wuyan kafafen yada labarai,”
- Inji Onanuga
Fadar shugaban kasa ta kuma gargadi kafafen yada labarai da jama’a su guji yada labarai marasa tabbas da ka iya jawo illa ga martabar ƙasa da kwanciyar hankali.
Sojoji sun yi watsi da rade-radin juyin mulki
A wani labarn, mun rahoto muku cewa rundunar tsaron Najeriya ta karyata cewa wasu sojoji sun yi shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Daraktan yada labaran DHQ, Birgediya-Janar Tukur Gusau, ya ce kama jami'an da aka yi ba ya da alaka da juyin mulki.
Rundunar sojin ta bukaci ‘yan ƙasa su yi watsi da jita-jitar da ke yawo, tana mai tabbatar da cewa sojoji suna da cikakken biyayya ga kundin tsarin mulki da tsarin dimokuradiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
