Tinubu Ya ba Hafsoshin Tsaro Aiki, Ya Bukaci Su Murkushe Barazanar da Ta Taso a Najeriya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama hafsoshin tsaro da matsayi a wani taro da aka shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Tinubu ya ce bullar kungiyoyin yan bindiga a Arewa ta Tsakiya da Arewa ta Yamma ne baranazar da ta damu gwamnatinsa
- Ya bukaci hafsoshin tsaron su tashi tsaye su tunkari duk wata barazana, domin yan Najeriya na son ganin zaman lafiya ya dawo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci hafsoshin tsaro da su tashi tsaye wajen magance barazanar tsaro da ke kara tasowa a sassa daban-daban na Najeriya.
Shugaba Tinubu ya fadi haka ne a yayin da yake karrama sababbin hafsoshin tsaro da matsayi fadar shugaban kasa da ke Abuja, yau Alhamis.

Source: Twitter
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
Abin da Tinubu ya fadawa hafsoshin tsaro
Da yake jawabi a taron, Tinubu ya ce barazanar tsaro na ci gaba da sauyawa da kuma bayyana a wasu siffofi, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da kuma wasu sassan Kudancin Najeirya.
“Barazanar tsaro na kara sauyawa, tana ƙaruwa, kuma abin da ke damun wannan gwamnati shi ne bullar sababbin ƙungiyoyin ’yan bindiga a yankunan da ke fama da tashin hankali.
"Ba za mu bari wadannan barazana su samu kafa ba. Dole mu yi gaggawa, mu murkushe su tun kafin su girma,” in ji Shugaban Ƙasa.
Tinubu ya ƙara da cewa ’yan Najeriya sun kosa su ga zaman lafiya da tsaro sun dawo, don haka ya bukaci hafsoshin tsaron su yi aikinsu da cikakken kishin ƙasa da sadaukarwa.
"Ina umartar ku a matsayinku na shugabannin rundunonin tsaron Najeriya da ku yi aiki da ƙwazo da jajircewa.
"Yan ƙasa suna buƙatar ganin sakamako, ba uzuri ba. Mun kagara mu fara murnar dawowar zaman lafiya."
- Bola Tinubu.
Tinubu ya daga darajar hafsoshin tsaro
Taron kara wa manyan shugabannin sojojin matsayi ya gudana ne a dakin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da ke fadar shugaban kasa.
A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya gudanar da sauye-sauye a tsarin tsaron ƙasar, inda ya nada sababbin hafsoshin tsaro, cewar rahoton Daily Trust.
A taron yau Alhamis, Olufemi Olatubosun Oluyede ya tashi daga matsayin Laftanar Janar ya koma Janar bayan nada shi a matsayin babban hafsan tsaro na kasa (CDS).

Source: Twitter
Shugaban hukumar leken asiri (DIA), Emmanuel Undiendeye Undiendeye ya tashi daga matsayin Manjo Janar, ya zama Laftanar Janar a rundunar sojoji.
Sauran su ne Hafsan Rundunar Sojijin Kasa, wanda ya tashi daga Manjo Janar ya zama Laftanar Janar Waidi Shaibu da Hafsan Sojojin Sama wanda ya tashi daga Air Vice Marshal, zuwa Air Marshal Kevin Aneke.

Kara karanta wannan
Bayan karbar bukatar Tinubu, majalisa ta sa lokacin tantance sababbin hafsoshin tsaro
Na karshe shi ne Rear Admiral, wanda yanzu ya zama Admiral Idi Abbas bayan nada shi a matsayin Hafsan Rundunar Sojojin Ruwa.
Hafsan sojojin sama ya yi alkwari
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF), Sunday Kelvin Aneke, ya yi alkawarin jagorantar runduna mai fasaha, ladabi, da kwarewa.
Air Vice Marshall din ya bayyana cewa zai jagoran rundunar da za ta hana ‘yan ta’adda sakat ballantana su samu damar shirya kai hare-hare kan jama'a
Aneke ya jaddada cewa manufarsa ita ce gina rundunar da za ta rika amsa kiran gaggawa a kan lokaci tare da kai hari daidai da ka’ida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

