Harajin 15%: Tinubu Ya Saka Kudin Shigo da Fetur da Dizil, Mai na iya Kara Tsada

Harajin 15%: Tinubu Ya Saka Kudin Shigo da Fetur da Dizil, Mai na iya Kara Tsada

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince da saka harajin shigo da man fetur da dizil na kashi 15 domin karfafa masana’antun cikin gida
  • Ana tunanin sabon tsarin zai iya haifar da karin farashin litar man fetur da N150, duk da cewa gwamnati ta ce tasirin ba zai wuce N100 ba
  • Shugaban kasa ya umurci hukumomin da abin ya shafa su fara aiwatar da tsarin nan take, maimakon jiran wa’adin kwanaki 30 da aka tsara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da kafa harajin shigo da man fetur da dizil na kashi 15 cikin 100.

Bayanai sun nuna cewa matakin zai iya janyo karin farashin man fetur da dizil a kasuwannin cikin gida.

Shugaba Bola Tinubu
Hoton shugaba Bola Tinubu da wani gidan mai. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Arise News ya ce matakin na zuwa ne bayan amincewar shugaba Bola Tinubu da shirin da ke da nufin tabbatar da tsaron makamashi da karfafa masana’antun tace mai na cikin gida.

Kara karanta wannan

Karfafa noma: Majalisa na son a daina shigo da shinkafa sosai daga ketare

An tura takardar ga babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, shugaban hukumar tattara haraji ta FIRS, Zacch Adedeji, da shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed.

Dalilan saka harajin 15% a shigo da mai

Takardar ta bayyana cewa ba domin kara kudin shiga aka kirkiri harajin ba, sai dai domin daidaita farashin shigo da mai tare da karfafa masana’antun cikin gida.

Gwamnati ta bayyana cewa manufar sabon harajin ita ce kare masana’antun tace mai na cikin gida, musamman bayan fara samar da man fetur da dizil daga matatar Dangote.

Matatar Dangote
Wani sashe na matatar Dangote da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Duk da haka, gwamnati ta ce farashin da ake amfani da shi a yanzu bai yi daidai da kudin da masana’antun ke kashewa wajen tacewa da rarraba mai ba.

A cewar gwamnati:

“Idan ba a daidaita wannan ba, za a ci gaba da samun rashin daidaito wanda zai iya lalata sababbin masana’antun da ke kokarin farfadowa.”

Don haka, an ce gwamnati na da nauyi biyu — kare masu amfani da mai daga tsadar rayuwa da kuma kare masana’antun cikin gida daga asara.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da sabon farashin kayan abinci a Najeriya

Tsarin aiwatar da dokar harajin mai

A cewar takardar, tsarin zai fara aiki nan take bayan amincewar shugaba Tinubu, duk da cewa a baya an tsara wa’adin kwanaki 30 don masu shigo da mai su daidaita kayansu.

The Cable ta rahoto cewa shugaban kasan ya rubuta cewa:

“An amince kamar yadda aka nema, a fara aiwatar da dokar nan take.”

An bayyana cewa kudin da za a tara za su shiga asusun gwamnati na musamman karkashin hukumar haraji ta NRS.

Haka kuma hukumar NMDPRA za ta tabbatar da cikakken biyan kudin kafin a samu izinin sauke kayan man fetur.

Aliko Dangote zai fadada matatar mai

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya fara shirin fadada matatarsa da ke jihar Legas.

A makon da ya wuce attajirin ya bayyana haka bayan wani zama na musamman da ya yi da manyan jami'ansa.

Dangote ya yi albishir da cewa zai dauki mutane da dama aiki kuma sama da shi 80 na wadanda za a dauka 'yan Najeriya ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng