Ana Neman CBN Ya Kawo Sababbin Takardun Kudin N10,000 da N20,000 a Najeriya
- Rahoton Quartus Economics ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaddamar da wasu takardun kudi
- An ji cewa rahoton ya ce faduwar darajar Naira ya sa takardar N1,000 ta zama marar kima sosai wajen sayayya
- Masanan sun ce tsoron cewa sababbin takardun kuɗi za su haifar da hauhawar farashi ra’ayi ne mai rauni
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Masana tattalin arziki daga Quartus Economics sun bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya fitar da sababin takardun kuɗi.
Rahoton ya nemi a samar da takardun N10,000 da N20,000 domin rage wahalar hada-hadar kuɗi da inganta sauƙin amfani da Naira.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa rahoton ya ce faduwar darajar Naira ta sanya takardar N1,000 – wacce ita ce mafi girma a yanzu – ta zama tamkar ba ta da wani tasiri wajen sayayya.

Kara karanta wannan
'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan neman sababbin takardun kudi
Masanan Quartus Economics sun ce idan aka kwatanta da shekarar 2005, lokacin da aka samar da N1,000 a karon farko, darajarta ta kai kusan Dala 7, amma a yau ta koma kasa sosai.
Sun ce hakan ya nuna yadda darajar Naira ta ragu sosai, inda yanzu ake buƙatar manyan takardu domin sauƙaƙe mu’amaloli musamman a kasuwanni da yankunan karkara.
Rahoton ya ƙara da cewa ganin yawancin ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu suna amfani da kuɗi kai tsaye, dole ne su riƙa ɗaukar babbar jaka cike da takardun N1,000 yayin hada-hada.
“Hakan yana da wahala, kuma yana rage ingancin harkokin kasuwanci,”
Inji rahoton
Batun hauhawar farashi da buga kuɗi
Rahoton ya karyata zargin cewa fitar da sababbin manyan takardun kuɗi zai haifar da hauhawar farashi.
A cewar masana, hauhawar farashi ba ta da alaƙa da girman takardar kuɗi:
“Kasashe da dama suna ƙara manyan takardun kuɗi domin kiyaye darajar kuɗin su bayan faduwar tattalin arziki, ba don ƙara hauhawar farashi ba.”

Kara karanta wannan
Akwai matsala: 'yan ta'adda da masu zanga zanga sun yi barazanar kai hari Majalisar Tarayya
Rahoton Quartus Economics ya kuma jaddada cewa tsadar bugawa da jigilar takardun ƙananan kuɗi ta zama matsala ga Babban Bankin Najeriya, lamarin da ke janyo asara mai yawa:
“Wajen buga takardun N200 ko N500 kawai, kudin jigila da tsaro sun fi darajar kuɗin kansa,”
Yunkuri kawo takardun kudi a baya
Rahoton ya tunatar da cewa CBN ta taɓa shirin fitar da takardar N5,000 a 2012 a lokacin tsohon gwamna Sanusi Lamido Sanusi, amma aka dakatar da shi bayan adawa daga jama’a.

Source: Twitter
Masana sun ce dalilan da suka sa aka tsara hakan a wancan lokaci sun fi dacewa a yau, ganin yadda darajar Naira ta ragu da kashi 94 cikin shekaru 20 da suka gabata.
A misali, rahoton ya ce farashin kilo 1 na shinkafa da ya ke N150 a 2005 yanzu ya kai N2,500, yayin da farashin tikitin jirgi daga Legas zuwa Abuja ya tashi daga N12,000 zuwa sama da N150,000.
Legit ta tattauna da dan kasuwa
A tattaunawa da Legit Hausa, wani dan kasuwa a Taraba, Muhammad Rahama ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kara takardun kudi.
Ya ce:
"A fahimta ta, idan aka kawo manyan kudi za a kara karya darajar Naira a Najeriya. Mun ga yadda kara takardun kudi ya jawo matsala a Zimbabwe."
"Ina ganin zai fi kyau a dawo tsarin 'cashless,' a ce daga N5 zuwa N200 ne na takardu. Sauran sai dai a tura su ta banki. Hakan zai rage ta'addanci a kasa."
Darajar Naira ta karu a kan Dala
A wani rahoton, kun ji cewa darajar kudin Najeriya (Naira) ta karu a kan kudin Amurka (Dala) a farkon makon nan.
Hakan na zuwa ne bayan tashin da Dalar Amurka ta yi a kan Naira sosai a kasuwar 'yan canjin kudi a Najeriya.
Masana sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen samawa 'yan Najeriya sauki musamman 'yan kasuwa da matafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
