Abin da Ya Sa Litar Fetur Ta Yi Tsada a Najeriya duk da Gangar Mai Ta Sauka a Kasuwar Duniya

Abin da Ya Sa Litar Fetur Ta Yi Tsada a Najeriya duk da Gangar Mai Ta Sauka a Kasuwar Duniya

  • Kungiyar dillalan mai ta IPMAN ta koka kan tashin farashin litar mai duk da gangar danyen mai ta sauka a kasuwar duniya
  • Bincike ya nuna cewa farashin kowace litar fetur ya kai N955 zuwa N960 a gidajen mai a birnin tarayya Abuja
  • Sai dai 'yan kasuwa na ganin tsadar na da nasaba da rashin ba su damar sayen fetur kai tsaye daga matatar Dangote

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Duk da raguwar farashin danyen mai a kasuwa ($65.25 a kowace ganga), farashin litar man fetur (PMS) ya kai N955 a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Shugaban ƙungiyar dillalan mai (IPMAN) na kasa, Alhaji Abubakar Maigandi, ne ya bayyana hakan da wata hira da aka yi da shi yau Laraba.

Gidan mai.
Hoton yadda ake hada-hadar man fetur a wani gidan mai a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Me ya jawo tsadar fetur a Najeriya?

Kara karanta wannan

Darajar Naira ta karu a kan Dala, Ana fatan 'yan Najeriya su samu sauki

Da yake tattaunawa da The Nation, shugaban IPMAN ya ce fetur ya yi tsada a gidajen mai ne saboda ba su da ikon sayen kaya kai tsaye daga matatar Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, dillalan mai ba su samun fetur kai tsaye daga matatar Dangote, sai dai su saya daga wasu manyan yan kasuwa masu rumbunan ajiya.

Abubakar Maigandi ya ce wadannan manyan dillalai ne kadai ke iya karbo fetur daga matatar Dangote ko kuma su shigo da shi daga kasashen ketare.

Rikicin Dangote da ƴan kasuwa

Idan ba ku manta ba, Matatar Dangote, wacce ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana, ta sanar shirinta na jigilar fetur zuwa gidajen mai kai tsaye kuma kyauta.

A cewar matatar, za ta fara wannan shiri ne daga ranar 15 ga Agusta, inda ta sayo sababbin tankokin mai masu amfani da gas (CNG) 4,000.

Sai dai ƙungiyoyi daban-daban masu hada-hadar fetur, kamar PENGASSAN, NOGASA, PETROAN, da NARTO, sun nuna adawa da wannan tsari.

A cewarsu, hakan zai sa direbobin manya motocin dakon mai su rasa ayyukansu, kuma barazana ce babba.

Binciken da aka yi a Abuja ya nuna cewa farashin man a gidajen mai ya kai N950 zuwa N960 a kowace lita, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Masu gidajen mai sun hango matsalar

Da yake karin bayani, shugaban IPMAN ya ce:

“Yan kasuwa masu gidajen mai ba su samun fetur kai tsaye daga Dangote. Wasu daga cikinmu muna saya ne daga rumbunan ajiya, wasu kuma ta hanyar shigo da kaya daga waje.”

Ya kara da cewa matatar Dangote ta sayar da kowace litar man fetur kan N877 a wurin lodi a ranar Talata da ta gabata.

Matatar Dangote.
Hoton wani bangaren matatar attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote da ke Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A nasa bangare, shugaban kungiyar PETROAN, Dr. Billy Hary, ya danganta hauhawar farashin fetur da rikicin da ya auku jan korar ma’aikatan da matatar Dangote ta yi.

“Har yanzu kasuwa ba ta murmure daga matsin lambar da rikicin da aka yi da Dangote ya jawo ba. Ba za mu iya cewa ga dalilin da ya sa farashin liatr mai ya tasbi ba."

Ana hasashen fetur zai yi araha

A wani labarin, kun ji cewa 'yan kasuwa da hukumar NMDPRA sun bayyana cewa farashin man fetur zai ci gaba da raguwa sakamakon fara aiki a matatar Warri.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote za ta zama mafi girma a duniya, 'yan Najeriya za su samu ayyuka

Masana da masu ruwa da tsaki a fannin sun nuna farin ciki da cewa ci gaban zai haifar da karin sauki ga al’umma ta fuskar farashi.

IPMAN ta bayyana cewa farashin mai zai ci gaba da sauka sakamakon kara yawan fetur da da ake tacewa a cikin gida Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262