Sababbin Hafsoshin Tsaro Sun San Matsayarsu bayan Tantance Su a Majalisa

Sababbin Hafsoshin Tsaro Sun San Matsayarsu bayan Tantance Su a Majalisa

  • Majalisar dattawan Najeriya ta tantance sababbin hafsoshin tsaro kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya bukata
  • Sanatoci sun kwashi dogon lokaci suna tattaunawa da hafsoshin kan abubuwan da suka shafi tsaro a kasar nan
  • Daga karshe majalisar ta tabbatar da nadin da Shugaba Tinubu ya yi musu don su jagoranci rundunonin sojojin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta kammala tantance sababbin hafsoshin tsaron da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada.

Majalisar dattawan ta tabbatar da nadin sababbin hafsoshin tsaron Shugaba Bola ya yi.

Majalisar dattawa ta amince da nadin sababin hafsoshin tsaro
Shugaba Bola Tinubu tare da sababbin hafsoshin tsaro Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa majalisar ta amince da nadin ne yayin zaman da ta gudanar a ranar Laraba, 29 ga watan Oktoban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka tabbatar da nadinsu sun hada da Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS), Manjo Janar Wahidi Shaibu a matsayin Babban Hafsan sojojin jasa (COAS).

Kara karanta wannan

Lakurawa: Sabon hafsan sojojin kasa ya sha alwashi kan 'yan ta'adda

Sauran su ne Rear Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan rundunar sojojin ruwa (CNS) da Air Marshal Kennedy Aneke a matsayin Babban Hafsan rundunar sojojin sama (CAS).

Sanatoci sun tattauna da hafsoshin tsaro

Jaridar Premium Times ta ce a yayin zaman, ‘yan majalisar sun tattauna da sababbin hafsoshin tsaro kan shirin da suke da shi na ƙarfafa haɗin gwiwa kan leken asiri, zamanantar da ayyukan soji, da kuma dawo da amincewar jama’a ga rundunonin tsaro.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanya batun tabbatar da su a kuri’ar murya, kuma dukkan ‘yan majalisar suka amince da ɗaukacin sunayen sababbin hafsoshin tsaron.

Akpabio ya yi jawabi a majalisa

Bayan tabbatarwar, Akpabio ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa zaben da ya yi na manyan hafsoshin da suka cancanta kuma masu kwarewa wajen sake fasalin tsaron kasa.

"Majalisa ta tattauna da waɗanda shugaban kasa ya gabatar don mukaman babban hafsan sojojin ruwa, babban hafsan sojojin sama, babban hafsan sojojin kasa da babban hafsan tsaro."
“Dukkan ‘yan majalisa sun yi tambayoyi daga kowace jiha, kuma waɗanda aka gabatar sun amsa dukkan tambayoyin yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

An fara: Majalisar Dattawa ta amince da nadin 1 daga cikin sababbin hafsoshin tsaro

- Godswill Akpabio

Majalisar dattawa ta tantance sababbin hafsoshin tsaro
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Ya ce tabbatar da sababbin hafsoshin tsaron na nuna wani amincewa da tsarin tsaro na gwamnatin Tinubu da kuma kudurin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.

"Ko da yake tsaro aikin kowa ne, mun ga cewa waɗannan hafsoshin sun cancanta sosai, kusan dukansu sun fito daga fagen daga a sassan daban-daban na duniya da sassa daban-daban na kasar nan."

- Godswill Akpabio

Akpabio ya kuma yabawa majalisar kan sadaukar da zamanta gabadaya domin aikin tantancewar, inda ya bayyana hakan a matsayin aikin kishin kasa.

Hafsan sojoji ya sha alwashi

A wani labarin kuma, hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu ya sha alwashi kan 'yan ta'addan kungiyar ta'addanci ta Lakurawa.

Manjo Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa a karkashin jaorancinsa, rundunar sojohi za ra ragargaji 'yab ta'addan Lakurawa.

Hafsan sojojin ya bayyana cewa tsaro ba abu ba ne mai arha, amma zai yi kokari wajen ganin ya rage karfin 'yan ta'adda a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng