Taraba: Rigima Ta Barke kan Mallakar Masallacin Juma’a na Izalah, an Rasa Rai
- An samu rigima a jihar Taraba kan wani babban masallacin Juma'a tsakanin kungiyar Izalah da dangin Danburam da ke garin Donga
- Rikicin ya barke ne a tsakaninsu kan mallakar masallacin garin, inda mutum ɗaya ya rasa ransa da kuma raunata wasu mutane
- Hukumar ‘yan sanda ta kira bangarorin biyu kafin rikicin, ta gargade su da gujewa tashin hankali, amma sun ki bin umarni suka kai farmaki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Donga, Taraba - An samu rikici mai muni tsakanin bangarori biyu masu adawa da juna kan mallakar babban masallacin Juma'a.
Rigimar ta barke ne a Donga da ke jihar Taraba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da lalata wasu kadarori bayan raunata mutane da dama.

Source: Facebook
Taraba: Yaushe aka yi rikicin kan masallacin?
Shafin Zagazola Makama da ke sharhi kan matsalolin tsaro ya tabbatar da haka a manhajar X a yau Laraba 29 ga watan Oktobar 2025.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya barke ne da yammacin Talata 28 ga watan Oktobar 2025 tsakanin mabiya Izalah da idangin Danburam.
An yada jita-jitar cewa mabiya kungiyar Izala Jos da dangin Danburam na shirin mamaye masallacin da ake rikici a kai a cikin garin Donga.
Wane mataki yan sanda suka dauka kan lamarin?
Wannan tashin hankali na zuwa ne duk da kokarin da yan sanda suka yi na tabbatar da cewa sun dakile shirin tayar da hankali da ake yi a yankin, cewar Daily Trust.
Bayan samun bayanan sirri, ’yan sanda sun kira bangarorin biyu domin gargadi, inda aka shawarce su da gujewa duk wani abu da zai kawo tashin hankali da lalata zaman lafiya.
Sai dai duk da matakin da aka dauka, kungiyoyin biyu sun fito da tarin mutane dauke da bindigogin hannu, adduna da duwatsu, wanda hakan ya haifar da arangama mai tsanani.

Source: Original
Wane hali ake ciki yanzu a Donga?
Rundunar yan sanda ta yi amfani da hayaki mai sanya hawaye, amma kafin a samu daidaito, matashi mai suna Biliya Zakari mai shekaru 20 daga unguwar Asibiti ya rasa ransa.
Haka kuma, an lalata wani ginin da ba karasa ba da ke kusa da masallacin yayin tashin hankalin, wanda ya jawo firgici a cikin al’umma da sanya fargaba kan makomar zaman lafiyar yankin.
Hukumomi sun tabbatar da cewa halin yanzu yankin ya dawo daidai, sai dai an kara tura jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da hana sake barkewar rikici.
Rigima ta barke kan limanci a masallacin Juma'a
A baya, kun ji cewa rigima ta kaure kan limanci a wani masallaci da ke yankin ƙaramar hukumar Agege a jihar Lagos bayan rasuwar babban liman, Malam Habib.
Shugaban ƙaramar hukumar Agege, Ganiyu Egunjobi ya ba da umarnin rufe masallacin nan take domin gudun tashin-tashina a yankin da tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce za a shirya zama da dukkan ɓangarorin biyu domin lalubo mafita da kuma magance yiwuwar tada zaune tsaye afin sake buɗe masallacin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


