An Fara: Majalisar Dattawa Ta Amince da Nadin 1 daga cikin Sababbin Hafsoshin Tsaro
- Majalisar Dattawa ta tantance sabon babban hafsan tsaro (CDS), Janar Olufemi Oluyede yau Laraba, 29 ga watan Oktoba, 2025
- Hakan ya biyo bayan daga matsayinsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi daga babban hafsan sojojin kasa zuwa babban hafsan tsaro
- Ana sa ran Sanatocin kasar za su tantance duka sababbin hafsoshin tsaron da aka nada bayan karbar wasikar Shugaba Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya - Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) bayan tantance shi a yau Laraba.
Janar Oluyede ya isa zauren Majalisar Dattawa tare da sauran hafsoshin tsaro da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada a makon jiya.

Source: Twitter
Majalisa ta fara tantance hafsoshin tsaro
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Majalisar Sattawa ta fara tantancewar ne da tsakar rana yau Laraba, 29 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar hafsoshin tsaron ta samu rakiyar Sanata Basheer Lado, Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin Majalisar Dattawa.
Tun farko shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da kudirin neman dakatar da Dokar Majalisa ta 12 wacce ke takaita shigowar baki.
Sanata Osita Ngwu ya mike ya goyi bayan bukatar Bamidele, daga nan aka bar hafsoshin tsaron suka shiga zauren Majalisar domin tantancewa.
Hafsoshin tsaron da za a tantance a Majalisa
Wadanda ake sa ran za a tantance sun haɗa da:
1. Laftanan Janar Olufemi Oluyede, Babban Hafsan Tsaro (CDS)
2. Manjo Janar Waheedi Shaibu, Babban Hafsan Sojojin Kasa (COAS)
3. Air Vice Marshal Kennedy Aneke, Babban Hafsan Sojan Sama (CAS)

Kara karanta wannan
Bayan karbar bukatar Tinubu, majalisa ta sa lokacin tantance sababbin hafsoshin tsaro
4. Rear Admiral Idi Abbas, Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa (CNS)
Kafin fara tantancewar, Sanata Bamidele ya tunatar majalisar cewa ta taba tantance Janar Oluyede, matsayin Babban Hafsan Sojojin Kasa (COAS).
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce duk sa haka yana da muhimmanci Oluyede ya yi bayanin kwarewarsa da abin da zai iya yi a sabon mukamin da aka nada shi.
Majalisa ta amince da nadin Janar Oluyede
Da ya hau mimbarin da aka tanada, Janar Oluyede ya bayyana cewa gogewar da ya samu a matsayin COAS ta kasance mai kalubale da kuma nasara.
"Kowa ya san kasafin da ake ware wa ba ya wadata, kayan aiki ma haka. Wannan ya sa yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda ya zama da wahala,” in ji shi.
Ya ce lokaci ya yi da ƙasa za ta fara ƙera nata kayan yaƙi da makamai, duba da tsadar shigo da su daga ƙasashen waje.
“Aikin soja na buƙatar sadaukarwa. Idan kana farar hula ka ga barazana, ana tsammanin ka ja da baya, amma soja yana shiga gaban barazana,” in ji Oluyede.
Bayan kammala bayani, Akpabio ya nemi ‘yan majalisa su ba Oluyede damar ruusnawa ya wuce kasancewar an taba tantance shi a baya, kuma sanatocin suka amince da hakan cikin hadin kai.
Bola Tinubu ya hadu da shugabannin sojoji
A baya ana da labari Bola Tinubu ya gana da sababbin hafsoshin tsaro a Aso Rock yayin da ake jita-jitar yin juyin mulki a kasar.
Hakan na zuwa ne awanni bayan ya kori su Christopher Musa, ya nada sababbin shugabannin sojoji lokacin da ake cikin dar-dar.
Bola Tinubu ya ja hankalin sabbabin hafsoshin tsaron, ya bukaci su nuna wa yan Najeriya sun cancanci rike wadannan mukamai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

