Sanusi II Ya Gargadi Tinubu kan Cin Bashi, Ya Tuna Abin da Ya Fadawa Buhari

Sanusi II Ya Gargadi Tinubu kan Cin Bashi, Ya Tuna Abin da Ya Fadawa Buhari

  • Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai kamata a rika ciwo bashi bayan cire tallafin mai ba
  • Ya yabawa gwamnati wajen daidaita tsarin musayar kudi da cire tallafin mai amma ya ce ba za a ga sakamako ba sai an sauya tafiya
  • Sanusi II ya ce matsalolin tattalin arzikin Najeriya sun samo asali ne daga rashin daidaito a manufofin gwamnati da kashe kudi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ciwo bashi.

Muhammadu Sanusi II ya ce bai kamata a rika ciwo bashi ba bayan cire tallafin mai da aka ce zai kara kudin shiga na gwamnati.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi korafi kan yawan kashe kudi da gwamnatin Tinubu ke yi

Sarki Sanusi II, Bola Tinubu
Sarki Muhammadu Sanusi II shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Masarautar Kano
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin taron Oxford Global Think Tank da aka gudanar a birnin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yaba da cire tallafin mai da kuma daidaita musayar kudi da gwamnatin ta yi, yana mai cewa duk da cewa matakan suna da zafi, amma suna da amfani matuka.

Sanusi II ya soki Tinubu kan cin bashi

Mai martaba Sanusi II ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ba zai haifar da wani ci gaba mai dorewa ba idan gwamnati ta ci gaba da neman lamuni daga waje.

Muhammadu Sanusi II ya ce:

“Idan ka daina biyan tallafi amma kana ci gaba da aro kudi, to ka toshe rami guda ne kana tono wani.
"Maganar gaskiya ita ce a duba yadda ake kashe kudin gwamnati da kuma sarrafa abin da aka adana daga cire tallafi.”

Sanusi II, wanda ya shugabanci Babban Bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014, ya ce irin wannan dabi’a ta sa Najeriya ke ta fama da koma bayan tattalin arziki tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Sabanin yadda ake zato, Sanusi II ya fadi dalilin Jonathan na fasa cire tallafi

Ya bayyana cewa ya gargadi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kan buga takardun kudi amma aka rika kallonsa a matsayin dan adawa.

Dalilin da ya haifar da matsalar tattali

Khalifa ya tuna cewa a shekarar 2012, ya yi gargadin cewa ba za a iya cigaba da biyan tallafin man fetur ba, amma siyasa ta hana daukar mataki.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya yayin wani jawabi a Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa Muhammadu Sanusi II ya ce:

“A lokacin, mun fada cewa tallafin mai zai durkusar da tattalin arziki, amma siyasa ta rinjayi gaskiya.
"Yanzu wadannan mutanen da suka yi zanga-zanga a baya sun gaji matsalar, kuma dole suka dauki matakin da ya dace.”

Ya kara da cewa rashin bin ingantattun shawarwari a baya ya janyo hauhawar farashi da raguwar darajar Naira.

'A rage kashe kudi,' Sanusi II ga Tinubu

A wani labarin, mun kawo muku cewa Muhammadu Sanusi II ya bukaci gwamnatin tarayya ta rage kashe kudin wajen gudanar da mulki.

Ya yaba da matakan da kwamitin tattalin arzikin shugaba Tinubu ke dauka wajen daidaita hauhawar farashi tare da cewa dole a takaita almubazzaranci da rashin gaskiya a gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ku daina": Sanusi II ya gano kuskuren da ministoci da hadimai suke yi ga shugaban kasa

A bayanin da ya yi, Sarki Sanusi II ya kara da cewa 'shi ya sa mutane irinmu suke zama ‘makiyan gwamnati’ saboda muna fadin gaskiya.'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng