Yan Bindiga Sun Farmaki Masu Sallah, Sun Yanke kan Wani da Ke Kokarin Tserewa

Yan Bindiga Sun Farmaki Masu Sallah, Sun Yanke kan Wani da Ke Kokarin Tserewa

  • ‘Yan bindiga sun kuma kai wani mummunan hari a jihar Katsina yayin da wasu yankuna ke ci gaba da zaman sulhu da su
  • Lamarin ya faru ne a garin Na’alma da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar inda suka farmaki masallata
  • Harin ya faru makonni kadan bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da ‘yan bindiga, abin da ya tayar da hankulan mazauna yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Malumfashi, Katsina - Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan farmaki a safiyar yau Laraba 29 ga watan Oktobar 2025.

Harin ya faru ne a garin Na’alma da ke cikin karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, yayin da jama’a ke cikin sallar Asuba.

Yan bindiga sun kai hari masallaci ana sallar asuba
Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Rahoton Bakatsine a dandalin X da ke kawo sharhi kan tsaro ya nuna cewa mutane da dama sun mutu yayin da wasu kuma suka jikkata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kakaba harajin miliyoyi a Sokoto ana shirin girbe amfanin gona

Ana ci gaba da kashe mutane a Katsina

Lamarin ya zo ne makonni kalilan bayan da wasu a yankunan jihar Katsina suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga, wanda ake sa ran zai dakike hare-hare.

Kananan hukumomi da dama sun tattauna da yan bindiga domin kawo karshen kai hare-hare da ake yi a jihar.

Duk haka, ana zargin maharan da rashin cika alkawari duba da yadda wasu ke ci gaba da kai hari kan al'umma tare da jawo asarar rayuka.

Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da matsalolin tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Wasu 'yan bindiga sun hallaka jama'a a Katsina

Majiyoyi sun tabbatar da cewa harin ya tarwatsa jama’ar da ke masallacin da kewaye yayin da ake ci gaba da zaman sulhu da yan bindiga.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa an sare kan wani mutum da yake kokarin tserewa daga harin abin da ya tayar da hankalin jama’a a yankin baki ɗaya.

A halin yanzu, ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba, domin jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba tukuna.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya kare manoma daga asara yayin da farashin abinci ya sauka

'Yan bindiga: Mutane sun bukaci taimakon gwamnati

Mazauna Malumfashi sun bayyana takaicinsu, suna cewa harin ya nuna rashin gaskiya daga bangaren ‘yan bindigan.

Mutane da dama na neman gwamnati ta dauki mataki mai tsauri domin kare rayukan jama’a da kuma dukiyoyinsu.

Wani dattijo a yankin ya ce:

“Mun yi tunanin an samu sauƙi bayan yarjejeniyar, amma yanzu abin ya yi muni. Muna fargabar abin da zai biyo baya.”

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wata sanarwa game da harin daga jami’an tsaro ko kuma gwamnati domin daukar matakin da ya dace.

'Yan bindiga sun sako mutane a Katsina

Mun ba ku labarin cewa al'ummar jihar Katsina na ci gaba da ganin amfanin sulhu bayan wasu tubabbun yan bindiga sun sako mutane.

'Yan bindigan sun saki mutum 19 da suka yi garkuwa da su a Katsina, bayan tattaunawar zaman lafiya karkashin shirin 'Operation Safe Corridor'.

Hukumomi suka ce ana duba lafiyar wadanda aka sako a cibiyar lafiya ta Haske, Sabuwa, kafin maida su wurin iyalansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.