Sojoji Sun Kama Darakta Janar da ake Zargi da Hannu a 'Shirin Juyin Mulki'
- Sojoji sun fara binciken wani Darakta-Janar na gwamnati da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki a Najeriya
- Rahotanni sun ce ya aika kuɗi masu yawa zuwa ga tsohon Ministan Mai, Timipre Sylva, wanda ake zargin ya tallafa wa shirin
- Rundunar soja ta kai samame gidan Sylva a Abuja, ta kama ɗan’uwansa da direbansa yayin da tsohon Ministan ke waje
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa jami’an leƙen asirin soja sun kama wani Darakta Janar na wata hukuma ta gwamnatin tarayya da ke yankin Kudu maso Kudu.
Sojojin sun cafke mutumin ne bisa zargin taimakawa wajen shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Punch cewa an kama daraktan ne saboda zargin aika makudan kuɗi zuwa ga tsohon Ministan Harkokin Mai, Mista Timipre Sylva.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kuma kyautata zaton yana cikin masu tallafawa shirin kifar da gwamnatin farar hula a karkashin Bola Ahmed Tinubu.
Sojoji sun yi kame a Kudu maso Gabas
Wata majiya ta shaida cewa Darakta Janar ya aika kuɗi masu yawa zuwa ga Timipre Sylva da ake zargin yana da alaka da shirin juyin mulki.
Wata majiya ta ce:
"Ana bincike kan yiwuwar cewa kuɗin na da nasaba da shirin juyin mulkin. Yanzu haka ana tambayarsa kan manufar aika kuɗi. Rahotanni sun nuna cewa an kai samame a gidan tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, da ke Abuja a ranar Asabar.
A yayin sunamen, jami’an tsaro suka kama ƙaninsa, Paga Sylva, wanda shi ne mai taimaka masa ta fuskar harkokin gida, tare da direbansa.
An ce Sylva, wanda jagora ne a jam’iyyar APC, yana ƙasar waje lokacin da jami’an binciken suka kai samame.
Wata majiya ta ce:
“Sylva yana shirin dawowa Najeriya kafin ya ji cewa an kama wasu daga cikin shugabannin juyin mulkin, hakan ya sa ya fasa dawowa.
Sojoji sun yi tsit kan batun juyin mulki
Sai dai har zuwa ranar Talata, ba a samu martani daga kakakin rundunar sojojin Najeriya, Manjo-Janar Markus Kangye, ko kakakin hulɗa da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar Tukur Gusau ba kan batun ba.

Source: Facebook
A baya, Birgediya-Janar Gusau ya bayyana a ranar 4 ga Oktoba cewa an tsare jami’ai 16 saboda laifuffukan karya doka da rashin ladabi a cikin rundunar.
Duk da haka, rahotannin jaridar SaharaReporters sun ce jami’an da aka kama daga mukamin Kyaftin har zuwa Birgediya Janar, suna tsare ne saboda zargin shirin kifar da gwamnati.
Ana zargin sojojin 16 ne ke shirya juyin mulki, kuma rundunar soja ta ɓoye gaskiya abin da ke faruwa saboda wasu dalilai.
Ana binciken shirin juyin mulki
A baya, mun wallafa cewa wasu majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamna daga yankin kudu na Najeriya yana cikin wadanda ake bincike bisa zargin a shirin juyin mulki.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Yan bindiga sama da 80 sun bakunci lahira da suka yi yunkurin shiga Kebbi
Ana zargin tsohon gwamnan na daga cikin wadanda ake kyautata zaton sun aika manyan kudi don tallafa wa wannan shirin, wanda aka tsara za a aiwatar a shekarar 2025.
A bangare guda, hedikwatar tsaron kasa (DHQ) ta cikin wata sanarwa ta karyata cewa an soke bikin Najeriya shekaru 65 saboda zargin yi wa Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

