Gwamnatin Tarayya za Ta Fadada Shirin Raba Tallafin Kudi ga Talakawa kai Tsaye

Gwamnatin Tarayya za Ta Fadada Shirin Raba Tallafin Kudi ga Talakawa kai Tsaye

  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta faɗaɗa shirin bayar da tallafin kuɗi kai tsaye don taimaka wa ƙarin talakawa da masu rauni a fadin ƙasar
  • Ministan kuɗi, Wale Edun, ya ce sama da gidaje miliyan 15 ke amfana yanzu, kuma akwai shirin ƙara yawan masu karɓar tallafin
  • Wale Edun bayyana cewa tsarin raba kudin yana gudana cikin gaskiya da bin doka domin tabbatar da cewa kowa ya karɓi hakkinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya za ta ƙara yawan gidaje da za su samu tallafin kuɗi kai tsaye zuwa fiye da miliyan 15 domin rage raɗaɗin da ake fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki.

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ne ya bayyana haka yayin taron Oxford Global Think Tank Leadership da ƙaddamar da littafi a Abuja, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi korafi kan yawan kashe kudi da gwamnatin Tinubu ke yi

Wale Edun, Bola Tinubu
Ministan kudi tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta rahoto ya ce shirin na daga cikin matakan gwamnati na tabbatar da cewa talakawa sun ji daɗin sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa a halin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnati ke raba tallafin kudi

Edun ya bayyana cewa shirin tallafin kuɗin kai tsaye yana gudana cikin gaskiya da tsari mai inganci wanda ke amfani da fasahar zamani.

Ya ce:

“Akwai yunƙurin tabbatar da cewa wahalar da sauye-sauyen tattalin arziki suka haifar sun ragu cikin gaggawa.
"Saboda haka aka samar da tsarin gaskiya da bin ƙa’ida domin biyan kuɗi kai tsaye ga gidaje miliyan 15.”

Ya ƙara da cewa tsarin yana amfani da bayanan jama'a inda ake da sunan kowane mutum da NIN, kuma ana biyan kuɗin ta asusun banki kai tsaye.

“A wasu wurare idan mutane suka ce ba su ji labarin wanda ya karɓi tallafin ba, muna kara duba wadanda muka turawa kudin, domin muna da adadinsu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama Darakta janar da ake zargi da hannu a 'shirin juyin mulki'

"Tsari ne da ake yinsa a bayyane.”

inji Wale Edun

Gwamnati za ta fadada raba tallafin kudi

Ministan ya ce gwamnati za ta ƙara yawan masu amfana da shirin zuwa matakan da za su shafi mutane da dama, domin tallafin ya isa ga jama’ar ƙasa baki ɗaya.

Ministan kudin Najeriya
Ministan kudin na kasa, Wale Edun. Hoto: @FinMinNigeria
Source: Getty Images

Ya kuma sanar da sabon shirin bunƙasa cigaban unguwanni wanda zai kai tallafi kai tsaye ga mutanen da ke cikin gundumomi 8,809 a fadin ƙananan hukumomi 774 na Najeriya.

“Wannan shirin zai taimaka wa ƙanana ’yan kasuwa da masana’antun gida."

- Inji Edun.

A nata jawabin, shugabar cibiyar Oxford Global Think Tank Leadership, Dr Arunma Oteh, ta bukaci gwamnati da ta ƙara saka jari a bangaren ilimi da abubuwan more rayuwa.

Darajar Naira ta karu a kan Dala

A wani rahoton, kun ji cewa darajar Naira ta dan karu a kan Dalar Amurka a ranar Talata, 28 ga Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Sabanin yadda ake zato, Sanusi II ya fadi dalilin Jonathan na fasa cire tallafi

Bayan karuwar da darajar Naira ta yi a kasuwar 'yan canji, masana sun ce hakan zai yi tasiri a harkokin 'yan Najeriya.

Masana sun bayyana cewa matafiya, masu shigo da kaya da masu fitar da abubuwa daga Najeriya zuwa ketare za su samun fa'idar karuwar darajar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng