Sabanin Yadda Ake Zato, Sanusi II Ya Fadi dalilin Jonathan na Fasa Cire Tallafi

Sabanin Yadda Ake Zato, Sanusi II Ya Fadi dalilin Jonathan na Fasa Cire Tallafi

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana dalilin da ya sa Goodluck Jonathan ya dakatar da cire tallafin man fetur a 2012
  • Basaraken ya ce ba wai maganar zanga-zanga da rashin amincewar yan Najeriya ba ne ya jawo aka fasa cire tallafin
  • Sanusi ya ce da gwamnati ta cire tallafin a lokacin, zafin da ake ji yanzu ba zai kai haka ba, yana yabawa Jonathan saboda jajircewarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi bayani kan fasa cire tallafin mai lokacin da yake gwamnan babban bankin Najeriya, CBN.

Sarkin ya bayyana dalilin da ya sa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shirin cire tallafin man fetur a shekarar 2012.

Sanusi ya sake magana kan cire tallafin mai
Sarki Sanusi a London yayin bikin kammala digirin digirgir. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

'Dalilin fasa cire tallafi a 2012' - Sanusi II

Kara karanta wannan

Sanusi II ya gargadi Tinubu kan cin bashi, ya tuna abin da ya fadawa Buhari

Rahoton Channels TV ya ce Sanusi II ya ce saboda tsoron harin kunar bakin wake daga Boko Haram ne, ba wai saboda zanga-zangar jama’a ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an yi wa manufar cire tallafin man da gwamnati ta ƙaddamar mummunar fahimta, inda tsarin tallafin a wancan lokaci ya zama dole wato gwamnati tana ɗaukar nauyin kare farashin mai ko da farashin danyen man ya tashi a kasuwa.

Sanusi ypa bayyana cewa wannan tsarin ya sa gwamnati ke biyan manyan kuɗaɗe don kiyaye farashin mai, har ta kai ga ana aro kuɗi ba wai don tallafin kawai ba, har ma don biyan riba kan bashi.

Ya ce:

"Daga amfani da kuɗaɗen shiga don tallafi, sai muka koma aro kuɗi don tallafi, daga baya kuma aro don biyan bashi. Wannan ya kai Najeriya ga matakin karyewar tattalin arziki.”

Sarkin ya ƙara da cewa, da gwamnatin Jonathan ta aiwatar da cire tallafin a 2012, to da zafin da ake fama da shi yanzu ba zai kai haka ba a wancan lokaci, cewar Punch.

“Da ‘yan Najeriya sun bari gwamnati ta cire tallafin a 2012, da akwai ɗan ciwo, amma da bai kai wannan azaba ta yau ba. Wannan shi ne farashin jinkirin gyara.”

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi korafi kan yawan kashe kudi da gwamnatin Tinubu ke yi

- Sarki Sanusi II

Sanusi ya fadi dalilin Jonathan na fasa cire tallafin mai
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Sarki Sanusi II. Hoto: Goodluck Jonathan, Sanusi II Dynasty.
Source: Facebook

Matsayar Sanusi II a 2012 kan cire tallafi

Ya bayyana cewa a lokacin yana CBN, sun yi lissafi kuma ya tsaya kai tsaye yana goyon bayan cire tallafin inda ya ce lokacin, idan an cire tallafi, hauhawar farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa 13 cikin 100.

Sanusi ya ƙara da cewa Jonathan ya dakatar da cikakken cire tallafin ne saboda tsoron harin Boko Haram.

Ya kara da cewa:

“Idan wani dan kunar bakin wake ya kai hari ga masu zanga-zanga a Lagos, Kano ko Kaduna, ya hallaka mutane 200, da magana ta wuce batun tallafi.
Saboda haka, zan ba Jonathan girmamawa saboda jajircewarsa. Dalilin da yasa ba a cire dauka ba kawai shi ne tsoron Boko Haram.”

Sarkin ya yaba wa Jonathan saboda jajircewarsa wajen aiwatar da gyaran tattalin arziki duk da matsin tsaro, yana mai cewa wannan ne ya nuna jarumtaka.

Gwamnatin Tinubu: Sanusi ya ba ministoci shawara

Kara karanta wannan

ADC ta 'gano' abin da ya sa gwamnatin Tinubu ke wasa da farashin abinci

Kun ji cewa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga ministoci da hadiman shugaban kasa, Bola Tinubu.

Sanusi II ya ja kunnen na kusa da shugaban kasar da su zama masu yi masa makauniyar biyayya da kwarzanta shi.

Basaraken ya bayyana cewa zama masu yi wa shugaban kasa kirari ba zai amfane su da komai ba face jawo musu tozarci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.