Gwamna Dikko Radda Ya Gwangwaje Sanata Hadi Sirika da Mukami a Katsina
- Gwamna Dikko Radda ya ba tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika mukami a Jami'ar Umaru Musa Yar'Adua
- Radda ya amince da nadinsa a matsayin shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar da ke jihar Katsina wanda zai fara aiki nan take
- Sirika, wanda tsohon minista ne a Najeriya, zai jagoranci ayyukan majalisar wajen inganta ci gaban jami’ar Ummaru Musa Yar’adua
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nada tsohon minista a Najeriya, Sanata Hadi Sirika mukami a gwamnatinsa.
Gwamna Radda ya ba Sirika kujerar matsayin shugaban majalisar gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke jihar Katsina.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya ba Sirika mukami a Katsina
Hakan na cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na @MSIngawa a yau Talata 28 ga watan Oktobar shekarar 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Injiniya M. S Ingawa mataimaki ne ga gwamnan Katsina wajen harkokin sadarwa na zamani.
Wannan nadi ya zo ne don fara wa’adin farko na shekaru biyar, wanda zai fara aiki daga ranar 24 ga watan Oktoba, shekara ta 2025.
Sanata Hadi Sirika, wanda ke rike da sarautar Marusan Katsina, Ministan Sufurin Jiragen Sama ne a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Nadinsa ya nuna amincewar Gwamna Radda da kwarewarsa wajen gudanar da al’amuran shugabanci da ilimi, musamman a bangaren raya cibiyoyin gwamnati.
Ana sa ran Sanata Sirika zai jagoranci kwamitin gudanarwa na jami’ar wajen inganta tsarin ilimi da ci gaban ayyukan da suka shafi dalibai da malamai.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna Dikko Radda ya nada Sanata Hadi Sirika (Marusan Katsina) a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina, na wa’adin farko na shekaru biyar, wanda zai fara aiki daga ranar 24 ga Oktoba, 2025."

Source: Facebook
Musabbabin nadin Hadi Sirika mukami a Katsina
Rahoton Vanguard ya ce Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, Mista Ibrahim Almu-Gafai, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa.
Ya ce, nadin ya fara aiki ne daga watan Oktoba wannan shekara ta 2025 wa'adinsa na ta farko kenan na tsawon shekaru biyar.
Almu-Gafai ya nakalto Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, yana cewa an nada Sirika ne bisa la’akari da hazakarsa da kyakkyawan aiki da ya nuna tsawon shekaru.
Ya ƙara da cewa:
“Gwamna ya bukaci wanda aka nada da ya yi amfani da gagarumin ƙwarewarsa wajen gudanar da aikinsa yadda ya dace.”
Hadi Sirika ya samu sarauta a Katsina
A baya, mun ba ku labarin cewa Masarautar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ta sanar da naɗin sababbin hakimai shida a faɗin jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren masarautar ya fitar ranar Asabar 3 ga watan Agustan 2025 wanda ɗan Gwamna Diko Raɗɗa yake cikin waɗanda aka naɗa a matsayin hakimai.
Haka zalika, tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya zama sabon Marusan Katsina, hakimin Shargalle a ƙaramar hukumar Dutsi da ke jihar Katsina.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


