ADC Ta ‘Gano’ Abin da Ya Sa Gwamnatin Tinubu Ke Wasa da Farashin Abinci

ADC Ta ‘Gano’ Abin da Ya Sa Gwamnatin Tinubu Ke Wasa da Farashin Abinci

  • Jam’iyyar ADC da ke adawa a Najeriya ta gano wani shiri da gwamnatin Bola Tinubu ke yi game da farashin kayan abinci
  • ADC ta zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da farashin abinci don neman farin jini kafin zaben 2027 da ake tunkara
  • Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya ce rahoton saukar farashin abinci karya ne da aka kirkira ta hanyar shigo da abinci daga waje

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar ADC ta nuna damuwa game da abubuwan da gwamnatin tarayya ke yi da ya shafi farashin kayan abinci a kasar.

Jam'iyyar ta zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da farashin abinci a matsayin dabarar siyasa don neman goyon baya kafin babban zaben 2027.

ADC ta taso gwamnatin Tinubu a gaba kan farashin abinci
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi tare da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Mallam Bolaji Abdullahi.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da TheCable ta samu wanda sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Litinin 27 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Sabanin yadda ake zato, Sanusi II ya fadi dalilin Jonathan na fasa cire tallafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta taso gwamnatin Tinubu a gaba

Bolaji Abdullahi ya ce ikirarin gwamnati cewa an samu ci gaba a samar da abinci a cikin gida ba gaskiya ba ne, ganin irin matsalolin da manoma ke fuskanta a sassa daban-daban na kasar.

Ya bayyana cewa saukar da ake gani a farashin abinci na yanzu “karya ce ta gwamnati,” wadda ta samo asali daga rangwamen haraji da aka bai wa masu shigo da abinci daga kasashen waje.

'Dan adawar ya ce abin da ake yi yana cutar da manoman cikin gida da ke fama da tsadar taki da rashin tsaro.

Ya ce:

“Raguwar farashin abinci da ake gani yanzu ba sakamakon ingantacciyar manufa ba ce, illa kawai sakamakon shigo da abinci daga kasashen waje wanda ke lalata kasuwar cikin gida.”

Ya kalubalanci yadda gwamnati ke cewa ana samun cigaba a harkar noma alhali manoma na gudu daga gonaki saboda hare-haren ‘yan bindiga da kuma tsadar kayan abinci.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya kare manoma daga asara yayin da farashin abinci ya sauka

“Ta ya ya za a ce noma yana inganta alhali yankunan karkara suna fama da ‘yan ta’adda, kuma farashin kayan noma ya zama abin da talaka ba zai iya dauka ba?”

- Bolaji Abdullahi

ADC ta ba Tinubu shawara kan inganta noma
Kakakin jam'iyyar ADC a Najeriya, Bolaji Abdullahi. Hoto: Mallam Bolaji Abdullahi.
Source: Facebook

ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da yin karya

Abdullahi ya kara da cewa abin da ke faruwa yanzu shi ne wata manufa ta siyasa domin baje kolin ci gaban karya, yayin da jama’a ke ci gaba da fama da yunwa da talauci.

Ya kuma zargi gwamnati da boye gaskiya, inda ya ce kin amincewar da take yi cewa ta fito da abinci daga ajiyar gwamnati ya nuna akwai tambayoyi kan haka, cewar Punch.

Ya kara da cewa:

“Idan ma za mu amince da wannan magana ta gwamnati, tambayar ita ce: me yasa gwamnati ke boye abinci a lokacin da jama’a ke mutuwa da yunwa? Wace irin gwamnati ce ke ajiye abinci a cikin yunwa?.”

Jam’iyyar ADC ta bukaci a sake duba tsarin noma gaba ɗaya domin mayar da hankali kan samar da abinci a cikin gida, tabbatar da daidaiton farashi da kuma tabbatar da tsaron abinci na dogon lokaci.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Farashin shinkafa ya fadi a Lagos

Kun ji cewa rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa farashin shinkafa ya fadi sosai a wasu kasuwannin Lagos.

‘Yan kasuwa sun koka kan asarar da suka yi, suna cewa sun sayi shinkafa da tsada amma yanzu suna sayarwa da araha.

Masana sun ce bude iyakoki da karin amfanin gona daga Arewa ne ya haifar da saukar farashin, amma farashin na iya tashi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.