Nasara daga Allah: Yan Bindiga Sama da 80 Sun Bakunci Lahira da Suka Yi Yunkurin Shiga Kebbi
- Jami'an tsaro sun yi nasarar kashe yan bindiga sama da 80 a lokacin da suka yi yunkurin shiga jihar Kebbi daga Zamfara
- Gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta tabbatar da aukuwr lamarin, ta ce sojoji sun yi masu lugude ta sama da kasa
- Mai ba gwamnan Kebbi shawara kan sadarwa, Abdullahi Zuru ya ce wannan nasara ta kara nuna kokarin gwamnati na dawo da zaman lafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Birnin Kebbi, jihar Kebbi - 'Yan bindiga sama da 80 sun gamu da ajalinsu yayin da suka gudo daga jihar Zamfara, suka yi yunkurin kutsawa cikin jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Mintuna 30 a tsakani, jirage sama 2 na rundunar sojoji sun yi hatsari, sun fada teku
Bayanai sun nuna cewa jami’an tsaro na hadin gwiwa sun halaka fiye da ’yan bindiga 80 lokacin da suka yi yunkurin kutsawa cikin jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara.

Source: Original
Jaridar Aminiya ta tattaro cewa jami'an tsaron sun samu wannan nasara ne a wani mummunan artabu da ya faru a dajin Makuku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun tarfa yan bindiga a Kebbi
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Najeriya sun tarfa yan bindigar ta sama da ƙasa a sansanoninsu da ke cikin dajin, inda suka yi masu ruwan wuta.
Bayan wannan luguden wuta, dakarun sojojin sun yi nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kebbi, Abdulrahman Zagga, ya fitar a Birnin Kebbi.
Bugu da kari, dakarun sojojin sun dakile wani hari da ’yan bindiga fiye da 400 suka kai garin Ribah, inda aka yi musu mummunar asara kafin su ja da baya.
Mai ba Gwamnan Kebbi shawara kan harkokin sadarwa da dabarun mulki, Abdullahi Idris Zuru, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sojoji sun kara zage dantse a Arewa
Ya kara da cewa nasarar ta nuna ƙwazon jami’an tsaro da jajircewarsu wajen yaƙi da ta’addanci a jihar Kebbi, in ji rahoton BBC Hausa.
“Dakarun sun yi aiki tukuru wajen hana ’yan bindigar samun damar shiga cikin Kebbi. Wannan samame wani ɓangare ne na ci gaba da yaki da ta’addanci da fashi da makami a sassan jihar,” in ji Zuru.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa sojojin Najeriya na ci gaba da kai hare-hare a dazuka da yankunan da ke kan iyaka, musamman a dajin Makuku, domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda.
Abdullahi Zuru ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi na ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro
A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun hallaka 'yan sa-kai na CJTF akalla guda takwas a wani farmaki da suka kai a jihar Zamfara.
Harin ya faru ne kusan makonni biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a masallaci, inda suka kashe mutane biyar ciki har da limami a kauyen Dandoto, yankin Tsafe.
Wani mazaunin Yandoton Daji, mai suna Aliyu Danlami, ya bayyana cewa al’ummar yankin sun shiga fargaba da rudani bayan harin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

