Shehu Sani Ya Fadi Kuskuren da Masu Neman Kafa Sababbin Jihohi Ke Yi a Yanzu

Shehu Sani Ya Fadi Kuskuren da Masu Neman Kafa Sababbin Jihohi Ke Yi a Yanzu

  • Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi magana kan masu neman a kirkiri sababbin jihohi a yankunansu a daidai wannan lokaci
  • Sanata Sani ya ce neman ƙirƙirar sababbin jihohi shekara daya kafin zaben 2027 ba shi da amfani kuma bata lokaci ne
  • Maganarsa ta jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin lamarin wata dabarar siyasa ce ta neman goyon baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi martani ga wasu da ke neman a kirkiri sababbin jihohi a Najeirya.

Sanata Shehu Sani ya yi watsi da kiraye-kirayen ƙirƙirar sababbin jihohi, yana mai cewa hakan bata lokaci ne matuka.

Shehu Sani ya magantu kan kirkirar sababbin jihohi
Sanata Shehu Sani da ya taba wakiltar Kaduna ta Tsakiya. Hoto: @ShehuSani, @NGRsenate.
Source: Twitter

Shehu Sani ya tabo maganar kirkirar sababbin jihohi

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, 28 ga Oktoba, Shehu Sani ya ce masu neman jihohi sababbi suna ɓata lokacinsu.

Kara karanta wannan

"Ku daina": Sanusi II ya gano kuskuren da ministoci da hadimai suke yi ga shugaban kasa

Shehu Sani ya yi magana kan lamarin musamman da yake ganin ana daf da shiga shekarar siyasa duba da karatowar zaben 2027.

“Mutanen da ke neman ƙirƙirar sabuwar jiha kusan shekara guda kafin zabe kawai suna ɓata lokaci ne.”

- Sanata Shehu Sani.

Maganar tasa ta zo ne yayin da ake ƙara matsa wa gwamnati da majalisa lamba daga yankuna daban-daban kan batun ƙirƙirar jihohi sababbi.

Kwamitin majalisa ya amince da kirkirar jihohi 6 a Najeriya
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisa, Tajudeen Abbas. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Twitter

Martanin mutane kan maganar Shehu Sani

Wasu daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana cewa gwamnatin yanzu na iya amincewa da hakan don dalilan siyasa.

Wani mai amfani da X, @shehu_mahdi, ya rubuta cewa:

“A karkashin APC, komai na ban mamaki yana iya faruwa, ka da ka yi mamaki idan suka yi gaggawar amincewa da kirkirar sababbin jihohi, mutane irin wadannan suna iya yin komai don cimma burinsu, amma daga bisani za su ruguje."

Haka kuma wani mai sharhi, @Aminuidaah, ya ce:

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

"Lamarin na iya zama dabarar yakin neman zabe, ganin babu wani ci gaba da gwamnati za ta nuna."

@_Designkreative kuwa ya danganta batun da yunƙurin jan hankalin yankin Kudu maso Gabas ta hanyar alkawarin ƙirƙirar jiha a gare su.

Ya tambaya cewa:

“Me ya sa sai yanzu kusa da zabe ake tunanin ƙirƙirar sabuwar jiha idan ba siyasa ba?”

Lamarin ya sake tayar da muhawara kan adalci a wakilci, musamman a yankin Kudu maso Gabas wanda ke da jihohi biyar kawai.

Wani mai amfani da X, @HonAmanzeMayor, ya ce:

"Duk wani yanki ban da Kudu maso Gabas da ke neman jiha yana neman kawo tsaiko ne kawai ga yankin domin samun damar yawan jihohi 6 kamar saura."

Za a kirkiri sabuwar jiha a Najeriya?

Kun ji cewa kwamitin majalisar tarayya na hadin guiwa kan gyaran kundin tsarin mulki ya amince da kafa sabuwar jiha a Najeriya.

An cimma matsayar ne yayin taron kwanaki biyu a Legas, inda aka tattauna kan bukatun karin sabuwar jiha a Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta amince da kirkirar karin jiha 1 a Najeriya

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya bukaci ‘yan majalisa su marawa kudirin baya domin tabbatar da adalci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.