Shugaba Tinubu Ya Tura Sunayen Sababbin Hafsoshin Tsaro ga Majalisar Dattawa

Shugaba Tinubu Ya Tura Sunayen Sababbin Hafsoshin Tsaro ga Majalisar Dattawa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawan Najeriya ta yi gaggawar amince wa da nadin sababbin hafsoshin tsaron da ya nada
  • Tinubu ya yi wannan roko ne a wasikar da ya aika Majalisar yau Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025 mai dauke da sunayen wadanda ya ke so ya nada
  • Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya karanta wasikar, ya bukaci sanatoci su amince a yi tantancewar gobe Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika sunayen sababbin hafsoshin tsaron da ya nada zuwa Majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

Takaitaccen bayani game da sababbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nada

Mai Girma Bola Tinubu ya tura wasika zuwa majalisar dattawa yana neman tantancewa da tabbatar da sababbin hafsoshin tsaro da ya nada kwanan nan.

Majalisar Dattawa.
Hoton zauren Majalisar Dattawan Najeriyada ke Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar shugaban ƙasa a zaman da aka gudanar a ranar Talata, kamar yadda The Cable ta kawo.

Sunayen hafsoshin tsaron Najeriya

A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaron Kasa (CDS) da Manjo Janar Waheedi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Sojojin Kasa (COS).

Haka nan wasikar ta sanar da Majlaisar cewa Tinubu ya nada Rear Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan Rundunar Sojojin Ruwa da Air Vice Marshal Kennedy Aneke a matsayin Babban Hafsan Sojojin Sama (CAS).

Sai kuma kuma na karshe, Manjo Janar Emmanuel Undiendeye wanda zai ci gaba da zama a matsayin Shugabar Hukumar Leken Asirin Tsaro ta Kasa.

Abin da Tinubu ya bukata daga Majalisa

A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya roki Majalisar Dattawan ta hanzarta tantance wadanda ya nada a matsayin jagororin rundunonin sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon janar ya fadi abin da zai faru a gidan soja bayan Tinubu ya yi sauye sauye

A cewar shugaban kasa, wannan matakin na neman tantancewa cikin gaggawa zai taimaka wajen karfafa tsarin tsaro da hadin kai tsakanin hukumomin a kokarin yaki da ta’addanci, ‘yan fashi, da sauran barazanar tsaro a fadin kasar nan.

'Yan Majalisa sun sa ranar tantancewa

Akpabio ya tura bukatar shugaban ƙasa zuwa Kwamitin Majalisar Dattawa na Gaba ɗaya domin gudanar da tantancewa da tabbatar da wadannan nade-nade a ranar Laraba.

“Ina roƙon sanatoci da su duba yiwuwar mu gudanar da tantancewar nan gobe (Laraba, 29 ga Oktoba, 2025) domin sababbin hafsoshin su fara aiki ba tare da bata lokaci ba, kada mu bar gibi a harkar tsaro,” in ji Akpabio.

Bayan hakan ne ‘yan majalisar dattawan suka amince da bukatar shugaban ƙasa cikin haɗin kai, bayan an kada kuri’a ta murya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Tinubu da hafsoshin tsaro.
Hoton Shugaba Tinubu tare da sababbin hafsoshin tsaro a Aso Rock Hoto: @Sundaydare
Source: Twitter

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro a Abuja

A baya, mun kawo maku rahoton cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi taron sirri da sababbin hafsoshin rundunonin sojojin Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Majiyoyi masu karfi sun nuna cewa ganawar na da nasaba da ƙoƙarin da ake yi don ƙarfafa tsarin tsaro da inganta aikin rundunonin sojoji a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sauya manyan sojoji zai iya jawo sama da Janar 60 su yi murabus a Najeriya

Fadar shugaban ƙasa dai ta bayyana cewa nadin sababbin hafsoshin tsaro wani muhimmin mataki ne na inganta tsarin tsaro da ayyukan rundunonin tsaro na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262