"Ku Daina": Sanusi II Ya Gano Kuskuren da Ministoci da Hadimai Suke Yi ga Shugaban Kasa
- Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya yi muhimmin kira ga ministoci da hadiman shugaban kasa
- Sanusi II ya ja kunnen na kusa da shugaban kasan kan zama masu yi masa makauniyar biyayya da kwarzanta shi
- Mai martaba ya bayyana cewa zama masu yi wa shugaban kasa kirari ba zai amfane su da komai face jawo musu tozarci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ja kunnen ministoci da hadiman shugaban kasa.
Sanusi II ya gargadi ministoci da hadiman shugaban kasa da su guji zama masu yi masa kirari, maimakon su ba shi shawarar gaskiya da za ta taimaka wajen ceto tattalin arzikin kasa.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Sanusi II ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Litinin a Abuja, yayin taron Oxford Global Think Tank Leadership Conference da kaddamar da wani litattafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen taron, Sanusi II da Atedo Peterside sun tattauna kan manufofin tattalin arziki da kalubalen shugabanci a Najeriya.
Sanusi II ya koka da shugabanci a Najeriya
A cikin jawabin nasa, Sanusi II ya ce matsalar shugabanci a Najeriya tana karuwa ne sakamakon son kai, saboda wadanda ke faɗin gaskiya ana ɗaukar su a matsayin makiyan gwamnati.
“Shugabanninmu suna sauraren waɗanda ke faɗa musu abin da suke son ji ne kawai."
“Najeriya tana da masu yi wa gwamnati kirari da yawa. Duk wanda ya faɗi gaskiya, ana ganin shi a matsayin makiyi.”
- Sanusi II
Ya soki dabi’ar yawan yabon shugabanni a tarurrukan gwamnati, yana mai cewa wannan hali yana hana fadin gaskiya da ci gaban kasa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.
“Idan ka shiga wurin taro kuma shugaban kasa yana nan. Abu na farko da mutane ke faɗi shi ne, ‘Mai girma shugaban kasa, muna godiya da jagorancinka. Allah ya albarkaci Najeriya ta hanyar sanyawa ka zama shugaba.’"
"Lokacin da suka gama wannan yabon, shawararsu kawai za a dauka."
"Amma idan ka fadi gaskiya kuma ka nuna kuskure, sai ace kai abokin gaba ne. Shi ya sa ake daukar mutane irinmu da Atedo Peterside a matsayin maƙiya gwamnati, saboda mutane ba sa son jin gaskiya.”
- Muhammadu Sanusi II

Source: Twitter
Wace shawara Sanusi II ya bada?
Ya yi kira ga ministoci da hadiman shugaban ƙasa su mayar da gaskiya da amana ginshiƙin aikinsu, yana mai jaddada cewa makauniyar biyayya da kirari ga shugabanni na cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban Najeriya.
“Waɗanda ke aiki tare da shugaban kasa su fahimci cewa ba amfaninsu ba ne idan suka zama masu yi masa kirari. Ka na tozarta kanka da ofishinka idan ka aikata hakan."
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya gargadi masu son rusa Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya aika da sakon gargadi ga masu son rusa Kano da tarihinta.
Sanusi II ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya rusa dadadden tarihin Kano wanda aka gina bisa gaskiya da adalci.
Mai martaba Sarkin ya ce idan ana maganar tarihin Kano, to ya samo asali ne daga ginshiƙan ilimi, addini, da kasuwanci da suka kafa tushe mai ƙarfi ga Arewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


