Masu Safarar Kwayoyi Sun Bude Wuta kan Jami'an NDLEA da Sojoji
- Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da dakarun sojoji sun fuskanci wani hari a jihar Edo
- Wasu masu fataucin miyagun kwayoyi ne suka budewa jami'an wuta lokacin da suka fita gudanar da aikinsu
- NDLEA ta bayyana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa ta yaki masu safarar miyagun kwayoyi a Edo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da sojoji sun fuskaci hari a jihar Edo.
Jami'an na NDLEA da sojojin sun fuskanci harin ne daga wajen masu fataucin kwayoyi a kauyen Ukpuje, karamar hukumar Owan ta Yamma ta jihar Edo.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamandan NDLEA na Edo, Mitchel Ofoyeju, ya fitar.

Kara karanta wannan
EFCC ta bayyana wasu 'yan kasuwa da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka farmaki jami'an NDLEA
Kwamandan na NDLEA ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 27 ga Oktoban 2025 yayin wani samamen hadin gwiwa domin lalata gonakin wiwi a yankin, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da labarin.
“Jami’anmu sun fuskanci harbi mai tsanani daga masu noma da fataucin kwayoyi yayin da suke shiga yankin Ukpuje."
- Mitchel Ofoyeju
Ya ce tawagar jami'an tsaron ta yi musayar wuta na ɗan lokaci kafin ta ja da baya domin guje wa rasa rayuka.
"Ɗaya daga cikin jami’anmu ya ji rauni bayan an jefa masa wani abu mai kaifi a jikinsa yayin harin, amma an kai shi asibiti kuma yana cikin koshin lafiya yanzu.
- Mitchel Ofoyeju
Mitchel Ofoyeju ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar noma da fataucin wiwi a jihar Edo, wadda ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan yankunan da ake samar da wiwi a Najeriya.
“Muna godiya cewa babu wanda ya rasa ransa. Wannan hari ba zai sa mu ja da baya ba wajen cika alkawarinmu na tsabtace Edo daga miyagun kwayoyi."
- Mitchel Ofoyeju

Source: Original
Hukumar NDLEA za ta kara azama
Ya ce NDLEA za ta kara tsananta kai farmaki a yankunan da ke da alaka da fataucin kwayoyi kamar Ukpuje, tare da tabbatar da cewa wadanda ke da hannu a harkar sun fuskanci hukunci.
Ofoyeju ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya a jihar.
Ya roki shugabannin al’umma da mazauna yankunan da su taimaka da bayanan sirri da za su taimaka wajen cafke masu fataucin kwayoyi.
NDLEA ta cafke tsoho mai safarar kwayoyi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar NDLEA sun samu nasarar hafke wani tsoho mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Anambra.
Tsohon mai suna Uchelue Ikechukwu wanda ke da shekara 70 a duniya, na daga cikin mutane shida da jami’an hukumar suka kama a wani samame a sassan jihar Anambra.
Jami'an na NDLEA sun cafke shi ne a Umudioka, karamar hukumar Dunukofia, da kilo 26.7 na miyagun kwayoyi da yake sayar wa ga matasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

