'Yan Bindiga Sun Kakaba Harajin Miliyoyi a Sokoto ana Shirin Girbe Amfanin Gona

'Yan Bindiga Sun Kakaba Harajin Miliyoyi a Sokoto ana Shirin Girbe Amfanin Gona

  • Al’ummar Bazar a Yabo ta jihar Sokoto sun roƙi gwamnatin jihar ta taimaka musu wajen biyan harajin da ‘yan bindiga suka kakaba musu
  • Mutanen yankin sun bayyana cewa rashin biyan harajin na iya janyo kai musu hari da kuma lalata amfanin gonarsu da ya kammala nuna
  • Wani mazaunin yankin, Alhaji Dauda Umar, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki sun sace mutane bakwai tare da sace kayayyaki masu daraja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Mazauna kauyen Bazar da kewaye a karamar hukumar Yabo ta jihar Sokoto sun roƙi gwamnatin jihar ta kawo musu ɗauki domin biyan harajin da ‘yan bindiga suka kakaba musu.

Sun ce idan ba su biya kudin ba, akwai yiwuwar ‘yan bindigar su kai musu hari ko su lalata amfanin gonarsu, lamarin da zai iya jefa su cikin tsananin talauci da yunwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga saman babura sun kai hari a Kano, an yi barna

Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu
Gwamnan Sokoto yayin wani taro. Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Leadership ta rahoto wasu mazauna yankin sun bayyana cewa sun gaji da zaman dar-dar sakamakon hare-hare da ‘yan bindiga ke kai musu lokaci zuwa lokaci duk da sanar da hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan bindiga sun kakaba haraji a Sokoto

Wani mazaunin yankin, Alhaji Dauda Umar, ya tabbatar wa manema labarai cewa gaskiya ne ‘yan bindigar sun bukaci harajin Naira miliyan 15 daga al’ummar Bazar.

Ya ce:

“Gaskiya ne ‘yan bindiga sun nemi mu biya harajin Naira miliyan 15, kuma sun yi barazanar kai mana hari idan ba mu biya ba.”

Alhaji Umar ya bayyana cewa bai da cikakken bayani kan lokacin da za su karɓi kudin, amma harajin ya riga ya tabbata kuma ana kokarin tara kudin domin guje wa tashin hankali.

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kai hari Bazar

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki a daren Juma’a da misalin ƙarfe 11:40 na dare suka bar yankin da ƙarfe 1:06 na safe.

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

A cewarsa:

“Sun tafi da mutane bakwai, amma daga baya suka sake sarkin kauyenmu da wasu mutane shida bayan sun gargade su da kada su sanar da abin da ya faru.”

Ya kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kwashe kayayyaki daga shaguna da darajarsu ta kai miliyoyin Naira, abin da ya kara jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali.

Matsalar tsaro ta dade a Bazar

Alhaji Umar ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ake kai musu hari ba, ya ce ‘yan bindigar sun saba zuwa saboda sun san yankin sosai.

Ya bayyana cewa sun sha sanar da jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda, amma matsalar ba ta gushe ba.

Mutane sun nemi taimakon gwamnan Sokoto

Punch ta rahoto cewa mutanen Bazar sun yi kira ga shugaban karamar hukumar Yabo da ya kai rahoton matsalar zuwa ga gwamnatin jihar Sokoto domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Sun roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su taimaka wajen kawo ƙarshen wannan matsalar da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.

Kara karanta wannan

Sauya kundin mulki: Majalisa ta fara bitar bukatun kirkirar jihohi 55 a Najeriya

Bulama ya yi magana kan tsaron Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa mai sharhi kan tsaro, Audu Bulama Bukarti ya yi magana kan sauya hafsoshin tsaro da aka yi.

Bulama Bukarti ya ce sauya hafsoshin tsaro da shugaba Bola Tinubu ya yi ba zai kawo karshen matsalar tsaron Najeriya ba.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki kan lamuran tsaro su sauya salon yaki da 'yan ta'adda a fadin kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng