"Ba a Kotu ba": Shugaban INEC Ya Fadi Inda Ya Kamata a Rika Lashe Zabe
- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya koka kan yadda ake samun shari'o'i da suka danganci zabe
- Farfesa Joash Amupitan ya bayyana cewa dole ne a rika lashe zabe a rumfunan zabe ba a yi nasara a cikin kotu ba
- Shugaban na INEC ya nuna cewa sai hakan ya faru ne za a iya cewa dimokuradaiyyar kasar nan ta girma
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sabon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya ce dole ne a daina barin kotuna su zama masu yanke sakamakon zaɓe a Najeriya.
Farfesa Joash Amupitan ya ce dole ne nasarar zaɓe ta fito daga rumfunan zabe, ba daga kotu ba.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce shugaban na INEC ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron shekara-shekara na 56 na kungiyar malaman shari'a ta Najeriya (NALT) da aka gudanar a Jami’ar Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan
"Abin kunya ne," An yi kaca kaca da shekaru 10 da Farfesa Mahmud Yakubu ya yi a INEC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amupitan na son a daina zuwa kotun zabe
Sabon shugaban na INEC wanda kwanan nan Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da shi, ya bayyana cewa lokacin yawaitar rigingimu a kotu kan zabubbuka ya zo karshe.
Farfesa Amupitan ya kuma yi alkawarin kawo ƙarshen yawaitar shari’o’in zaɓe kafin kada kuri'a, da ya dade yana janyo cikas ga tsarin zabe a kasar nan, rahoton Daily Post ya tabbatar da labarin.
Ya bayyana cewa kafin zaɓen 2023, an gabatar da fiye da shari’o’i 1,000 na rikicin zaɓe, abin da ya kira da cewa ba dimokuraɗiyya ba ce hakan.
“Idan jam’iyyun siyasa za su girmama kundin tsarin mulkinsu, su bi dokar zaɓe da kuma kundin tsarin mulkin kasa, to, wannan tarin shari’o’in zaɓen zai kare."
- Farfesa Joash Amupitan
Farfesa Amupitan ya ce manufarsa ita ce a mayar da doka makamin kawo gyara, ba rikici ba.
“Buri na shi ne idan muka samu daidaito a cikin doka, ko wanda ya sha kaye shi ne zai fara taya wanda ya yi nasara murna. A lokacin ne za mu ce dimokuraɗiyyarmu ta girma."
- Farfesa Joash Amupitan
Shugaban INEC ya mika bukata ga majalisa
Ya bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta karfafa dokokin zabe domin tabbatar da gaskiya da dimokuraɗiyya cikin gida a cikin jam’iyyun siyasa.

Source: Twitter
Farfesa Amupitan ya amince cewa rage yawan shari’o’in zabe ba zai faranta wa kowa rai ba, amma ya ce dawo da amincewar jama’a ga tsarin zabe shi ne abu mafi muhimmanci.
“Ba za mu ci gaba da barin kotuna su rika yanke mana hukunci kan zaɓe ba. Dole ne a ci zaɓe a rumfunan zabe, ba a cikin kotu ba."
- Farfesa Joash Amupitan
Shugaban INEC ya bada mukami
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya nada mai magana da yawun bakinsa.
Farfesa Joash Amupitan ya nada tsohon editan jaridar Punch, Adedayo Oketola, a matsayin mai magana da yawunsa.

Kara karanta wannan
Nnamdi Kanu: Jagoran IPOB ya kasa kare kansa a gaban kotu, ya mika sabuwar bukata
Adedayo Oketola, wanda dan jarida ne mai kwarewa kuma gwarzon da ya ci kyaututtuka da dama, yana da gogewa ta shekaru 20 a harkar jarida, tattalin arziki, da shugabanci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
