ADC ta Bukaci Tinubu Ya Kare Manoma daga Asara yayin da Farashin Abinci Ya Sauka

ADC ta Bukaci Tinubu Ya Kare Manoma daga Asara yayin da Farashin Abinci Ya Sauka

  • Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Tarayya da yin amfani da wahalar abinci domin cimma muradun siyasa
  • Ta ce gwamnatin na yada bayanan karya kan karuwar abinci alhali manoma da dama sun tsere daga gonaki
  • Jam’iyyar ta nemi a sake fasalin tsarin noma domin kare manoma da tabbatar da daidaiton farashi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa zargin cewa tana amfani da matsalar abinci a matsayin makami na siyasa.

Jam’iyyar ta ce ikirarin gwamnati na cewa samar da abinci a gida ya karu karya ne, domin yawancin manoma musamman a Arewacin kasar sun tsere daga gonakinsu saboda hare-haren ’yan bindiga.

Bolaji Abdullahi, Bola Tinubu
Shugaba Tinubu da kakakin jam'iyyar ADC. Hoto: Bayo Onanuga|Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Tribune ta wallafa cewa ADC ta ce waɗanda suka rage suna noma ma suna fama da tsadar taki da sauran kayan amfanin gona, abin da ya kara tabarbarewar yanayin abinci a kasar.

Kara karanta wannan

Za a zamantar da ilmi a Najeriya, malamai za su daina taba alli daga 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar ADC kan cewa abinci ya sauka

ADC ta ce ba a fahimtar dalilin da ya sa gwamnati ke boye kayan abinci da aka shigo da su yayin da miliyoyin ’yan kasa ke fama da yunwa ba.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa.

Jam’iyyar ta bayyana hakan a matsayin wani salo na “yin siyasa da talauci” domin amfani da wahalar da jama’a ke ciki wajen samun karbuwa.

Ta ce abin takaici ne yadda gwamnati ke ta yada labaran cewa farashin abinci ya sauka, alhali abin da manoma da talakawa ke fuskanta daban ne da abin da gwamnati ke ikirari.

ADC ta soki ikirarin karuwar samar da abinci

Jam’iyyar ta bayyana cewa rahotannin da ake yadawa game da karuwar samar da abinci karya ne da gwamnati ta kirkira don boye gazawarta.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda

Kayana abinci a Najeriya
Yadda ake sayar da kayan abinci a wata kasuwa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar jam’iyyar, wannan rahoto na dogaro ne da shigo da abinci daga kasashen waje ta hanyar yin rangwamen haraji, wanda ya jawo farashin abinci mai arha a kasuwa.

ADC ta ce matakin na cutar da manoman cikin gida:

“Wannan ba wata hujja bace ta ingantacciyar manufar tattalin arziki ko karuwar samar da abinci a cikin gida,”

ADC ta nemi a kare manoma daga asara

ADC ta ce abin mamaki ne yadda gwamnati ke ikirarin karuwar samar da abinci a daidai lokacin da manoma ke tserewa daga yankunan karkara saboda hare-haren ’yan bindiga.

“Ta yaya samar da abinci zai karu alhali ana fama da tashe-tashen hankula a karkara kuma farashin taki da kayan noma ya fi karfin yawancin manoma?”

- Inji kakakin ADC

ADC ta bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba manufofin ta na noma domin kare manoma, daidaita farashin abinci.

Legit ta tattauna da Aliyu AKT

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi korafi kan yawan kashe kudi da gwamnatin Tinubu ke yi

A tattaunawa da wani masani kuma mai harkar kayan abinci, Aliyu AKT ya nuna damuwa kan yadda manoma ke asara a yanzu, amma ya ce za su samu mafita a gaba.

Aliyu ya ce:

"Hakika, Gwamnatin Najeriya na fitar da alkaluma a kan sauki kayan masarufi. To Amma, an gudu ba a tsira ba.
"Sabida ana cutar da manoma. ToAmma hanzari ba gudu, dama ance duk hannun daya kirka riba, zai kirga faduwa.
"Manoma zasu fanshe nan gaba kadan. Misali, yau farashin masara a kasuwar duniya bata kasa da N50,000. Kaga ko babu yaddan za a yi manyan masana'antu suje kasar waje bayan kayan na sauki a cikin gida.
"Adaidai wannan gaban ne farashin kaya zai haura."
"Muna kiran da babban murya, gwamnatin Najeriya da ta duba harkan nan, a duba farashin takin zamani da sauran kayan da gona. Idan ba haka ba, tattalin arzikin Najeriya zai tabu."

Fadar shugaban kasa ta ce abinci ya sauka

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta fitar da sabon farashin kayan abinci a kasuwannin Najeriya.

Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sunday Dare ne ya fitar da sanarwa kan yadda ya ce an samu sauki sosai.

Kara karanta wannan

ADC ta 'gano' abin da ya sa gwamnatin Tinubu ke wasa da farashin abinci

Dare ya bayyana cewa farashin shinkafa, masara, wake, dawa, manja garin kwaki da sauransu duk sun yi kasa sosai a bana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng