'Yan Bindiga Saman Babura Sun Kai Hari a Kano, an Yi Barna
- An shiga jimami bayan 'yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kano
- Miyagun 'yan bindigan sun kai farmakin ne a karamar hukumar Shanono inda suka yi kisa tare da sace dabbobi masu yawa
- Majiyoyi sun bayyana 'yan bindigan sun zo a kan babura inda suka rika harbi domin firgita mutane kafin daga bisani su kwashe kayayyaki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - ’Yan bindiga da ake zargin sun fito daga Katsina sun kai hari a kauyen Faruruwa da ke karamar hukumar Shanono a jihar Kano.
Miyagun 'yan bindgan sun kashe mutum daya tare da yin awon gaba da dabbobin al’umma.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yamma a ranar Talata, 27 watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kai farmaki a Kano
Maharan wadanda ake kyautata zaton sun zo da babura fiye da 25 sun dira a kauyen, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
A cewar wasu ganau, kowane babur ɗaya yana ɗauke maharan kusan mutum uku dauke da bindigogi, inda suka rika harbi a iska don tsoratar da jama’a kafin su fara farma shaguna da sace dabbobi.
“Sun fara ne da kai hari kan wani shagon wayoyi, daga nan suka balle wasu shaguna da dama suka kwashe wayoyi da sauran kayayyaki masu daraja."
- Wani mazaunin garin
An rasa rai da 'yan bindiga suka shiga kauye
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, maharan sun kashe mutum ɗaya mai suna Lado a unguwar Yanlanba yayin da suka kawo harin.
“Sun mamaye garin, suka kwashe kayan jama’a da kuma shanunsu. Kafin ‘yan sanda su iso wurin, tuni maharan suka tsere."
Majiyar ta kara da cewa yanzu al’ummar yankin suna cikin tsananin tsoro sakamakon sake kawo hare-hare, don haka suka roki hukumomin tsaro da su kara yawan jami’an tsaro a yankin domin hana sake faruwar irin haka.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
“Muna rayuwa cikin tsoro. Mutanen Faruruwa suna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo dauki cikin gaggawa kafin lamarin ya fi haka muni."
- Wata majiya

Source: Original
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Sai dai majiyoyin yankin sun tabbatar da cewa an riga an birne gawar wanda aka kashe bisa koyarwar addinin Musulunci.
Wannan harin ya kara tsananta damuwa kan yaduwar ayyukan ‘yan bindiga daga jihar Katsina da wasu makwabtan jihohi zuwa sassan Kano.
'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun samu nasarar cafke wasu 'yan bindiga yayin wani samame da suka kai.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, brahim Adamu Bakori, an cafke mutanen da ake zargin ne a daren ranar Juma'a, 24 ga watan Oktoban 2025.
Ibrahim Adamu Bakori ya ce an gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri daga mazauna kauyen Farin Ruwa a karamar hukumar Shanono.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
