Sarkin Hausawan Makurdi, Rayyanu Sangami ya Rasu Wata 1 da Samun Mulki

Sarkin Hausawan Makurdi, Rayyanu Sangami ya Rasu Wata 1 da Samun Mulki

  • An tabbatar da rasuwar Sarkin Hausawan Makurdi, Alhaji Rayyanu Sangami, bayan gajeriyar rashin lafiya a asibitin ABU, Zariya
  • An birne marigayin a Makurdi ranar Asabar da safe bisa tsarin Musulunci bayan an kawo gawarsa daga Zariya, jihar Kaduna
  • Kungiyar Izala da 'yan siyasa daga ciki da wajen jihar sun yi ta'aziyya ga iyalan marigayin da al’ummar Hausawa a Benue

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue – Sarkin Hausawan Makurdi, Alhaji Rayyanu Sangami, ya rasu bayan gajeriyar jinya a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, Jihar Kaduna.

Ya rasu ne a ranar Asabar, 25, Oktoba, 2025, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, inda aka ce an birne shi a Makurdi da misalin ƙarfe 11:20 na safe bisa ka’idar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

2027: Sule Lamido zai nemi takarar shugaban jam'iyyar PDP na kasa

Alhaji Rayyanu Sangami Sarkin Hausawan Makurdi
Sarkin Hausawan Makurdi da ya rasu, Alhaji Rayyanu Sangami. Hoto: Rayyan Shehu Odoje
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar Alhaji Rayyanu Sangami ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Hausawa ya rasu wata 1 da nada shi

Marigayi Sangami ya hau gadon sarautar Sarkin Hausawan Makurdi ne a ranar 20, Satumba, 2025, kafin Allah ya yi masa rasuwa bayan kwana 35 da nadin nasa.

Wani sako da aka wallafa a Instagram, ya nuna cewa nadin sarautar da aka masa ya samu halartar manyan mutane a jihar, ciki har da shugaban majalisar dokoki.

Kungiyar Hausawan Najeriya ta yi ta’aziyya

Kungiyar Hausawan Najeriya ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma Hausawan Makurdi bisa wannan babban rashi.

A cikin sakon da kakakin ƙungiyar, Abdulrahman Umar Adamu ya fitar a ranar 27, Oktoba, 2025, ya bayyana cewa marigayin bai wuce kwana 35 a kan kujerar sarautarsa ba kafin Allah ya karɓi ransa.

Ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, an kashe miyagu kusan 100 a Kebbi

“Allah ya ji kansa, ya yi masa rahama, kuma ya baiwa iyalansa da al’ummarsa haƙurin jure wannan rashi mai nauyi.”

Izala ta yi ta’aziyyar Sarkin Hausawa

Shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya nuna jimaminsa bisa rasuwar marigayin wanda ya kasance ɗaya daga cikin jigo-jigon ƙungiyar JIBWIS a jihar Benue.

A cikin sakon ta’aziyyar da ya wallafa a Facebook, ya ce:

“Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa Sarkin Hausawan Makurdi kuma jigo a ƙungiyar JIBWIS, Alhaji Rayyanu Sangami wanda Allah Ya yi masa rasuwa a safiyar yau ɗin nan.”

Dr Jalo ya kuma miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da shugabannin ƙungiyar Izala a jihar Benue, yana roƙon Allah ya jikansa da rahama.

Alhai Rayyanu Sangami
Lokacin nada Rayyanu Sangami Sarkin Hausawa. Hoto: Muhammad Aliyu Almaliky
Source: Facebook

Jana’izar marigayin ta samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa, malaman addini, kungiyoyi daban-daban daga sassan jihar.

Mufti Haji Umer ya rasu a Habasha

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban majalisar malaman kasar Habasha, Mufti Haji Umer ya rasu.

Gwamnatin kasar ta nuna damuwa da rasuwarsa tare da bayyana ayyukan alheri da ya jagoranta a lokacin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji

A Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin tare da rokon Allah ya sanya shi a Aljannar Firdausi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng