Gwamna Ya Nada Sarkin Zaar na Farko a Tarihi, Rigima Ta Barke kan Wanda Aka Nada

Gwamna Ya Nada Sarkin Zaar na Farko a Tarihi, Rigima Ta Barke kan Wanda Aka Nada

  • Nada Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (mai ritaya) a matsayin Sarkin Zaar na farko ya tayar da kura a jihar Bauchi
  • Gwamnatin Bauchi ta bayyana cewa an bi matakai da ka'idojin wajen zaben Sarkin Zaar, masarautar da aka kafa kwanan nan
  • Al'ummar Sayawa da suka jima suna fafutukar kafa masarautar sun yi fatali da wanda aka nada, sun roki gwamna ya duba muradan jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Najeriya – Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da nadin Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (mai ritaya) a matsayin Sarkin Zaar (watau Gung-Zaar) na farko a tarihi.

Kara karanta wannan

Mintuna 30 a tsakani, jirage sama 2 na rundunar sojoji sun yi hatsari, sun fada teku

Masarautar Zaar na daya daga cikin masarautu 13 da gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta kirkiro a makonnin da suka gabata.

Sarkin Zaar da Gwamna Bala na Bauchi.
Hoton sabon Sarkin Zaar da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi Hoto: Sen Bala Mohammed
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce sanarwar nadin ta fito ne daga Misis Khadija Danladi Hassan Kobi, jami’ar yada labarai ta ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu ta jihar Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bauchi ta nada Sarkin Zaar

A cewar sanarwar da aka fitar yau Litinin, an nada sabon Sarkin ne bisa tanade-tanaden Dokar Masarautar Zaar ta shekarar 2025.

Tun farko dai gwamnatin Bauchi ta fitar da sanarwar ba da iznin neman wadanda suka cancanta da su shiga takara neman kujerar sarautar.

Khadijah Kobi ta bayyana cewa gwamnati ta karbi takardun yan takara bakwai, aka tantance su, inda daga bisani mutane uku suka janye, suka bar ’yan takara huɗu da suka fafata a zaben Sarkin.

“Bayan kammala zaben Sarkin Zaar, Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (Mai ritaya) ne ya samu nasara.
"Za a miƙa shi ga gwamna domin amincewa da kuma nadinsa a hukumance a matsayin Gung-Zaar na farko na Masarautar Zaar,” in ji ta.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, an kashe miyagu kusan 100 a Kebbi

Nadin Sarkin Zaar na farko ya tada kura

Sai dai rahotanni sun nuna cewa wannan ci gaba ya haifar da zanga-zanga a Karamar Hukumar Tafawa Balewa, inda wasu mutanen Sayawa suka bayyana rashin amincewarsu da matakin gwamnati.

Masu zanga-zangar sun ce ba su amince da nadin wani ba, suna masu jaddada cewa Air Commodore Ishaku Komo (mai ritaya) ne “Sarkin da ya dace da al’adunsu."

Sun bukaci Gwamna Bala Mohammed da gwamnatin Jihar Bauchi da su girmama muradun jama’a tare da guje wa nadin wanda al’umma ba su kauna.

Gwamna Bala Mohammed.
Hoton Gwamna Bala Mohammed a gidan gwamnatinsa da ke Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Kafa Masarautar Zaar da kuma zaɓen Sarkin na farko, ya nuna babban ci gaba a gwagwarmayar da al’ummar Sayawa suka shafe shekaru suna yi don samun matsayi na kansu a tsarin masarautun gargajiyar Jihar Bauchi.

Gwamma Bala ya nada yayansa a sarauta

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan Bauchi ya nada yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin masarautar Duguri da aka ƙirƙira kwanan nan.

Kara karanta wannan

Turaki ya kara fuskantar matsala a shirin zama shugaban PDP na kasa

Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Aminu Hammayo, ne ya mika takardar naɗe a madadin Gwamnan a fadar Sarkin Duguri.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnan Bala Mohammed ya kirkiri sababbin masarautu domin inganta shugabanci da samar da ingantaccen shugabanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262