Ganduje, Matarsa da Wasu Mutum 6 Sun Kawo Tsaiko a Zaman Babbar Kotun Kano
- Lauyoyin tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje da wadanda ake tuhuma da karkatar da kudin Kano sun kawo tsaiko a zaman Kotu
- Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta shigar kara tana tuhumar Ganduje da wasu mutum bakwai
- A zaman Babbar Kotun Kano yau Litinin, wadanda ake tuhuma sun gaza tura takardun da suka wajaba a kansu kafin fara shari'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Najeriya – An samu tsaiko a zaman sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mutum bakwai a babbar kotun Kano.
Gwamnatin Kano ce ta maka tsohon shugaban APC, Ganduje a kotu bisa zargin cin hanci da karkatar da kuɗaɗen gwamnati a lokacin mulkinsa tsakanin 2015 zuwa 2023.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa lauyoyin Ganduje da sauran wadanda ake tuhuma ne suka kawo tsaiko a zaman yau Litinin saboda gaza gabatar sa takardun da suka wajaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta maka Ganduje a kotu
Gwamnatin Jihar Kano na tuhumar mutane takwas da aikata laifuffuka 11 da suka haɗa da cin hanci, haɗin baki, karkatar da dukiyar jama’a da suka kai Biliyoyin Naira, in ji TVC News.
A cikin waɗanda ake tuhuma tare da Ganduje akwai matarsa, Hafsat Umar Ganduje, da ɗansa Umar Abdullahi Umar.
Sauran wadanda ake tuhuma a karar su ne, Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad, da kamfanonin Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.
Me ya kawo tsaiko a zaman kotun Kano?
A yayin zaman kotu na yau Litinin, lauyan gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fara gabatar da shaidu.
Sai dai ya roƙi kotun da ta yi watsi da roƙon wadanda ake tuhuma tare da bada damar ci gaba da shari’ar ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai lauyar da ke kare Ganduje, matarsa, da ɗansa, Misia Lydia Oluwakemi-Oyewo, ta shaida wa kotu cewa ba su shirya ba, saboda takardun da tura ba su samu isarwa ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba.
Ta ce:
“Mai girma mai shari'a ba mu shirya ba tukuna. Mun tura takardu ga ɓangarori amma ba su samu isa ba. Don haka muna neman a dage zaman zuwa wani lokaci.”
Haka zalika lauyoyin sauran wadanda ake tuhuma sun roki kotu ta dage zaman domin ba au damar shiryawa yaddaya kamata.

Source: Facebook
Kotu ta dage shari'ar Ganduje
A hukuncinta, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta umarci dukkan ɓangarorin da su tabbatar sun mika dukkan takardunsu kafin zaman gaba, don kaucewa jinkiri mara dalili.
Kotun ta daga shari’ar zuwa ranar 26 ga Nuwamba, 2025, domin ci gaba da sauraron wannan shari'a.
Dalilin kai karar Ganduje a kotu
A baya, kun ji cewa gwamnatin Kano ta gurfanar da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ‘ya’yansa biyu da wasu mutane a gaban babbar kotun jihar.
Gwamnatin Abba ta dauki wannan mataki ne kan Ganduje da iyalansa bisa zargin almundahanar N4.4bn wanda ɓangaren tsohon gwamnan ya musanta.
An shigar da karar a ranar 13 ga Oktoba, 2025, inda gwamnati ke neman dawo da 20% hannun jari da kudin da ake zargin an karkatar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


