Nnamdi Kanu: Jagoran IPOB Ya Kasa Kare Kansa a gaban Kotu, Ya Mika Sabuwar Bukata

Nnamdi Kanu: Jagoran IPOB Ya Kasa Kare Kansa a gaban Kotu, Ya Mika Sabuwar Bukata

  • Shari'ar da ake yi wa jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ta dauki sabon salo a ranar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025
  • Jagoran na IPOB ya hakikance a gaban kotu cewa babu wata sahihiyar tuhuma da ake yi masa kan zargin ta'addanci
  • Hakan na zuwa ne dai bayan a baya ya bukaci kotun ta ba shi lokaci domin ya yi cikakken nazari tun da ya kori lauyoyinsa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta, Nnamdi Kanu, da ke tsare, ya kasa fara kare kansa a shari'ar da ake yi masa.

Nnamdi Kanu ya janye shawarar da ya yanke ta kiran shaidu a shari’ar da ake yi masa kan zargin ta’addanci.

Nnamdi Kanu ya kasa fara kare kansa
Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: @DejiAdesogan
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Nnamdi Kanu ya kasa fara kare kansa ne yayin zaman kotu na ranar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun dai ta dage zaman shari’ar na ranar 24 ga Oktoba, zuwa 27 ga Oktoba, domin Kanu ya fara kare kansa.

A farkon watan Oktoba, Kanu ya rubuta wa kotu wasika, inda ya nuna niyyarsa ta kiran shaidu da kuma neman a ba shi lokaci don nazarin fayil ɗin shari’arsa.

Meyasa Kanu ya ki kare kansa?

Amma a zaman kotun ranar Litinin, Kanu ya ce ya gama duba takardun shari’ar kuma ya gano cewa babu wata sahihiyar tuhuma da ake yi masa.

Ya bayyana cewa tun da ya gamsu babu wata sahihiyar tuhuma a kansa kuma ana yi masa shari'ar da ba ta dace ba a fuskar doka, babu bukatar ya fara kare kansa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da labarin.

“Ku taya ni gode wa Allah. Na duba fayil ɗin shari’ata gaba ɗaya, babu wata tuhuma da ta dace da ni."
“Babu wata doka a Najeriya da masu shigar da kara za su dogara da ita kan tuhumar da ake yi mini. Idan akwai, to ina rokon mai shari’a ya karanta min.”

Kara karanta wannan

ADC ta aika sako mai zafi ga Tinubu kan sauya hafsoshin tsaro

- Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu ya ci gaba da cewa tunda babu wata tuhuma bisa doka, ba ya ganin akwai bukatar ya fara kare kansa, saboda haka ya nemi kotun ta sake shi ko ta bada belinsa.

Alkali ya ba Kanu shawara

Alkalin kotun, mai shari’a James Omotosho, ya shawarce shi da ya rubuta hujjar da yake da ita a rubuce, sannan ya mikawa lauyoyin gwamnati.

Kanu ya ce ba a yi masa sahihiyar tuhuma
Nnamdi Kanu tare da lauyoyi a kotu Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Ya kuma ba shi shawarar ya tuntuɓi masana a harkar shari’ar laifuffuka domin fahimtar tasirin wannan mataki da ya ɗauka.

Kotun ta daga shari’ar zuwa ranakun 4, 5, da 6 ga watan Nuwamba, domin karɓar bayanan karshe daga ɓangarorin biyu dangane da matsayar wanda ake kara cewa hujjojin da aka gabatar ba su kai a tuhume shi ba, ko kuma ya fara kare kansa.

Wike ya magantu kan zama shaidan Kanu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi magana kan zama shaidan Nnamdi Kanu a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Wike ya fadi sharadin zama shaidan shugaban IPOB a kotu

Wike ya bayyana cewa ba zai je gaban kotun ba kawai don sunansa ya fita a cijin jarida cewa yana cikin masu bada shaida.

Ministan ya bayyana cewa zai bi umarnin kotu ne kawai idan an kira shi da sammaci na doka don bayar da shaida ko gabatar da hujja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng