Kungiyar Amnesty Int'l Ta Yi Magana da Hisbah Ta Kama Masu Shirin 'Auren Jinsi' a Kano
- Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi tir da wani aikin da hukumar Hisbah ta yi a Kano
- A sakon da kungiyar ta fitar, ta ce babu dalilin da zai sa jami'an Hisbah su kama matasan da ake zargi da shirin auren jinsi
- Amnesty Int'l ta ce abin kunya ne a rika kama mutane bisa yadda suka sa kaya ko irin askin da suka yi a kansu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar Amnesty Int'l reshen Najeriya ta yi Allah-wadai da kama wasu mutane 25 da hukumar Hisbah ta Kano ta yi a ranar Juma’a, 25 ga Oktoba, 2025.
Jami'an hukumar Hisbah sun yi kamen ne bisa zarginsu da halartar bikin ƴan luwadi da kuma shirya auren maza da maza.

Source: Facebook
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, kungiyar ta ce aikin da hukumar Hisbah ta yi ya saba da dokar kare hakkin dan adam.
Amnesty Int'l ta soki aikin Hisbah a Kano
Kungiyar Amnesty Int'l ta bayyana cewa bai dace hukumar Hisbah ta riƙa shiga hakkin mutane ba saboda wasu dalilai nata.
A cewar sanarwar kungiyar:
“Dole ne hukumar Hisbah ta daina waɗannan mummunan samame da saba wa doka da take yi, tana amfani da ƙa’idoji wajen tsoratar da mutane bisa zargin aikata lalata."
"Abin takaici ne cewa Hisbah tana kama mutane bisa yadda suka saka kaya ko yadda suka gyara gashinsu.”

Source: Original
Kungiyar ta ƙara da cewa:
“Shiga cikin sirrin mutane da zargin cewa suna aikata laifi abu ne da bai dace ba. Babu wanda ya kamata a kama saboda ya yi ko kuma abin da ake zato na yanayin sha'awar jinsinsa.”
Martanin jama’a ga Amnesty Int'l
Bayan wannan sakin da Amnesty International ta fitar, wasu masu biniyarta sun yi martani da zafafan kalamai, inda da dama suka nuna rashin amincewa da matsayar ƙungiyar.
@Ngncitizen1 ya ce:
“Ku tafi can ku faɗa musu da lasifika, mtsww. Me ya shafi ku da rayuwar mutane? Ina roƙon gwamnati ta ɗauki mataki mai tsauri.”
@UthmanM70789626 ya ce:
"Dokokin Najeriya, al’adu da dabi’unmu duk suna ƙin wannan abin da kuke karewa. Ku ɗauki wannan ajandar banza ku tafi da ita wajen Najeriya.”
Wani Kabiru da ya zanta da Legit ya bayyana cewa:
"Wato Amnesty ta fitsare kafarta. Wannan Isah Sunusi ya fitsare ƙafarsa."
Amnesty Int'l ta shawarci Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Amnesty International, ta sake yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta soke duk wani tanadi na hukuncin kisa daga tsarin shari’a.
Kungiyar ta yi kiran a wani taro da aka shirya a Abuja, tare da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Faransa a Najeriya, domin tunawa da Ranar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya.
Barbara Magaji — wacce manaja ce a Amnesty — ta bayyana cewa babu wata hujja ko bincike da ya nuna cewa hukuncin kisa yana rage yawan manyan laifuka kamar fashi,
Asali: Legit.ng

