Gwamnan Bauchi Ya Yi wa Masu Suka Martani kan Nada Dan Uwansa Sarki
- Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya kai ziyara garinsa na Duguri, inda ya girmama sabon Sarki, Adamu Mohammed
- Bala Mohammed ya bayyana cewa danginsa tun fil azal suna daga cikin zuriyar masu mulkin sarautar garin Duguri
- Ya ce nadin sabon sarkin ya biyo bayan shawarwari masu kyau, tare da nufin karfafa zaman lafiya da ci gaban al’umma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya kai ziyara garinsa na Duguri domin girmama sabon sarkin yankin kuma dan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed Duguri.
A yayin ziyarar, Gwamnan ya bayyana farin cikinsa kan yadda sabon sarkin ya fara aiki bisa tsari da kuma hadin kan al’umma.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanin da gwamnan ya yi ne a wani sako da hadiminsa, Lawan Muazu Bauchi ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta cigaba da goyon bayan sababbin masarautun da aka kirkiro domin kara kusantar da mulki ga al’umma.
“Dama sarautar tamu ce” — Gwamna Bala
Yayin jawabi a wajen ziyarar, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa danginsu tun daga kaka da kakanni suna daga cikin gidan sarautar Duguri.
A wani bidiyo da shafin Kauran Bauchi Media TV ya wallafa a Facebook, gwamnan ya ce:
“Dama sarautar ta mu ce. Ko in ba dan uwa na ne ko in ba dana, watakila ma da ina nan da sai in nema da shi, sai dai duk abin da yayunmu suke nema ba mu shiga.”
Gwamna Bala ya bayyana cewa ya je Duguri ne domin nuna jin dadi da godiya ga Allah bisa wannan rana mai tarihi.
Ya ce:
“Na je domin in nuna farin ciki. Idan na ce ban ji dadi ba, to na yi karya.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin hadin kai
Sanata Bala ya bayyana cewa gwamnatin sa tana aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sababbin masarautu da aka kirkira a jihar.
Ya ce ana yin hakan ne domin ganin an samu karuwar ci gaban tattalin arziki da walwalar jama’a a jihar.
Haka kuma, ya bukaci sabon sarkin da ya kasance mai hada kan jama’a, tare da yin aiki da masu ruwa da tsaki don bunkasa harkokin rayuwa a Duguri.

Source: Facebook
Sabon sarkin ya gode wa gwamna Bala
A nasa jawabin, sabon sarkin Duguri, mai martaba Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya bayyana godiya ta musamman ga gwamna Bala Mohammed bisa amincewar gwamnati da nadin nasa.
Ya ce zai ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen aiwatar da manufofinta, musamman na ci gaban yankunan karkara da wanzar da zaman lafiya.
Manya kasa sun hallara taro Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya jagoranci taron tattalin arziki na jihar.
An gudanar da taron ne domin jawo hankalin masu zuba jari game da albarkatun kasa da jihar Bauchi ke da su.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo sun hallara taron.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


