Matatar Dangote za Ta Zama Mafi Girma a Duniya, 'Yan Najeriya za Su Samu Ayyuka
- Matatar Dangote da ke Legas ta sanar da karin karfin tace mai daga ganga 650,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a rana
- Aliko Dangote ya ce wannan mataki yana goyon bayan manufar shugaba Bola Ahmed Tinubu ta habaka Najeriya
- Fadada matatar za ta samar da dubban ayyukan yi da kuma rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas – Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya sanar da cewa matatar shi za ta kara karfin tace mai daga ganga 650,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a rana.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa hakan zai mayar da matatar shi da ke Najeriya mafi girma a duniya.

Source: Getty Images
A sakon da ya wallafa a Facebook, Dangote ya ce karin tace man da matatar za ta yi a yanzu zai zarce matatar Jamnagar da ke kasar Indiya, wacce a yanzu ita ce mafi girma a duniya.
Dangote ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lagos a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa yunkurin yana nuna kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin Najeriya tare da goyon bayan manufar gwamnatin Bola Tinubu.
Dangote ya yaba wa Bola Tinubu
Aliko Dangote ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ba shi goyon baya wajen sayar masa da danyen mai da Naira.
Ya ce hakan ya jawo sauyi a bangaren man fetur na kasa ta hanyar karfafa tace shi a cikin gida da fitar da kayayyakin man da aka gama tacewa zuwa kasashen waje.
Dangote ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalolin da suka janyo tsaiko a ayyukan matatar.
Tashar Channels TV ta rahoto cewa ya buga misali da rikicin da matatar ta yi da kungiyar ma’aikatan mai da gas da yunkurin lalata wasu sassa na injunan matatar.
Matatar Dangote za ta dauki 'yan Najeriya aiki
Dangote ya bayyana cewa kara yawan tace man zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da man kasashen waje, tare da adana daruruwan biliyoyin daloli da ake kashewa wajen sayo man.
Ya ce aikin zai samar da ayyukan yi sama da 65,000 a lokacin gina sababbin sassa, tare da bude damammaki ga masana’antun cikin gida da masu sana’o’i.
Dangote ya kara da cewa fiye da kashi 85 na ma’aikatan da za su yi aikin fadada matatar za su kasance ’yan Najeriya ne.

Source: UGC
Dangote ya tabbatar da cewa ba za a samu karancin mai a Najeriya ba yayin bukukuwan karshen shekara, duk da tashin farashin man a kasuwannin duniya.
Ya kuma yi kira ga masu rike da sauran lasisin gina matatun mai 30 a kasar su hada kai da shi wajen mayar da Najeriya cibiyar tace mai ta Afirka.
Dangote zai sayar da hannun jari
A wani labarin, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi magana kan wani shiri na sayar da hannun jarin matatarsa.
Ya ce za a fitar da kashi 10 na hannun jarin masana’antar a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya a shekara mai zuwa.
Attajirin Afrikan ya yi magana kan yiwuwar karawa kamfanin man Najeriya na NNPCL yawan hannun jari a matatar.
Asali: Legit.ng


