An Dauke Wutar Lantarki a Arewa yayin da Mahara Suka Lalata Kayayyakin TCN
- Wasu bata gari sun rusa babban turken wuta na T347da ke kan layin Gombe–Damaturu, wanda ya jefa Borno da Yobe cikin duhu
- Kamfanin TCN ya tabbatar da cewa injiniyoyi sun fara gina sabon turken wutar domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa
- TCN ya ce tashar ba da wutar gaggawa ta Maiduguri (MEPP) na taimakawa wajen samar da wuta ga kamfanin rarraba wuta na Yola
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno — Mazauna jihohin Borno da Yobe sun fada duhu bayan wani sabon harin mabarnata kan turken wutar lantarki na kasa, wanda ya katse samar da wuta a yankin Arewa maso Gabas.
Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da cewa bata garin sun rusa turken wuta na T347, daya daga cikin manyan hasumiyoyin 330kV da ke kan layin Gombe–Damaturu.

Source: Getty Images
Borno, Yobe sun fada cikin duhu
A wata sanarwa da Ndidi Mbah, babbar manajan hulda da jama’a na TCN ta fitar, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, da karfe 5:46 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndidi Mbah ta bayyana cewa tawagar bincike ta gano cewa an yanke kafafun turken wutar, wanda hakan ya sa ya karkace ya fadi a gefe guda.
“Lamarin ya haifar da katsewar wutar lantarki a Maiduguri, Damaturu da wasu garuruwan makwabta,” in ji Mbah.
TCN ta dauki mataki kan lalacewar wuta
Kamfanin TCN ya ce an dauki matakan gaggawa domin rage tasirin daukewar wutar, yana mai cewa:
“A halin yanzu, tashar ba da wutar gaggawa ta Maiduguri ce ke samar da wuta ta hannun kamfanin rarraba wuta na Yola, musamman ga manyan layukan 33kV kamar Beneshiek, Damasak, Bama, jami’ar Maiduguri, Monguno da sauran wurare."
- Ndidi Mbah.
Haka kuma, Damaturu da unguwanni makwabta za su ci gaba da samun wutar lantarki ta karamar tashar wuta ta Potiskum har sai an kammala gyaran.
Mbah ta kara da cewa injiniyoyin kamfanin sun isa wurin don fara aikin sake gina turken wutar da rushe.
“Injiniyoyinmu suna aiki ba dare ba rana domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa,” in ji Mbah..

Source: Getty Images
An la'anci masu lalata wutar lantarki
Kamfanin TCN ya bayyana harin a matsayin “zagon kasa da ke cutar da ci gaban Najeriya,” yana mai cewa:
“Abin takaici ne yadda ake ci gaba da samun maimaituwar irin wannan hrin, lamarin yana jinkirta cigaban kasa. Wadannan kayayyaki mallakin al’umma ne, don haka dole ne mu kare su."
Ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu sa ido su kuma rinka sanar da jami’an tsaro ko ofishin TCN mafi kusa idan sun ga wani abu da bai dace ba.
Tushen wutar lantarkin Najeriya ya lalace
A wani labari, mun ruwaito cewa, a ranar 10 ga watan Satumba, 2025, tushen wutar lantarki na Najeriya ya sake lalacewa a fadin kasar nan.
Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) ya fitar da sanarwa, da ta tabbatar da katsewar wuta a yankunan da yake kula da su.
An rahoto cewa, karfin wutar lantarki ya ragu zuwa megawatt 50 kacal ga kamfanonin rarraba wutar lantarki na ƙasar yayin da injiniyoyi suke gyara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


