'Ka da Ku Biya Kuɗin Fansa': Gargaɗin Malami idan Ƴan Bindiga Suka Sace Shi
- Malamin addini a jihar Plateau ya yi magana kan masu garkuwa da mutane inda ya yi wa mabiyansa gargadi kan biyan kudin fansa
- Fasto Ezekiel Dachomo ya ce idan an sace shi, kada a biya fansa, yana mai cewa jininsa zai haifar da yaki na ’yantar da Kiristoci
- Malamin ya bayyana cewa ya yarda da haɗarin da yake ciki game da kisan gilla a Arewa, musamman waɗanda ke kai wa Kiristoci hari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Wani malamin addini daga jihar Plateau ya ja kunnen mabiyansa kan biyan kudin fansa idan yan bindiga sun sace shi.
Fasto Ezekiel Dachomo, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan bidiyonsa da ke yawo, inda ya ce kar a biya fansa idan an sace shi.

Source: Facebook
Gargadin Fasto kan biya masa kudin fansa
A bidiyon da Vanguard ta gano, Dachomo ya bayyana cewa mutuwarsa za ta haifar da yaki da zai kai ga ’yantar da Kiristoci a Najeriya daga zalunci da kashe-kashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya bayyana haka yayin da ake ci gaba da kisan al'umma a yankunan jihar Plateau wanda ke kara tayar da hankulan al'umma.
Ya ce:
“Mun nuna musu jin kai da ƙauna amma ba su gane ba. Na gaya wa iyalina, idan an sace ni, kar kowa ya tara kuɗi.
“Mutuwata za ta yi magana, jini na zai tayar da yaki da zai kawo ’yanci ga Kiristoci.”

Source: Original
Fasto ya sadaukar da rayuwarsa kan gaskiya
Faston, wanda ke da matsayi a coci a Plateau, ya ce ya yarda ya sadaukar da rayuwarsa domin yin magana game da rikice-rikicen Arewa da kisan Kiristoci.
“Ranar nan tana zuwa, idan suka sace ni, zan ce su kashe ni da wuri, domin ba wanda zai kawo ko kobo."
- Fasto Ezekiel Dachomo
Kafin wannan, Dachomo ya fitar da wani bidiyo da ke nuna jana’izar mutanen da aka kashe a Heipang, kusa da Jos a jihar Plateau.
Ya ce bidiyon hujja ce da za ta nuna wa duniya cewa ana kashe Kiristoci a Arewa, kuma ba za a iya musun hakan ba, cewar Daily Post.
Maganganu sun biyo bayan kalaman Fasto
Malamin ya ce yana jin wajibi ne ya nuna gaskiyar abin da ke faruwa don kada a manta da irin waɗannan laifuffuka.
Maganganunsa sun haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke nuna damuwa da kuma goyon baya ga jarumtarsa.
Wasu sun ce yana fuskantar barazana saboda magana kan kisan gilla, yayin da wasu ke yaba masa da gaskiya da tsoron Allah wajen kare Kiristoci.
Yan bindiga sun hallaka Fasto a Plateau
Kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyukan Suwa da Ding’ak a Mushere, Bokkos a jihar Plateau, inda suka kashe mutum uku.
Kefas Mallai ya tabbatar da mutuwar Fasto Gideon Katings, Sunday Ringkang da Meshach Bukata, yayin da wasu suka ji rauni.
Gwamna Caleb Mutfwang ya kira harin “kisan kiyashi” da yunƙurin kwace ƙasa, yana tabbatar da hadin gwiwa da jami’an tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

