'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan Bindiga a Kano bayan Fara Kai Hare Hare

'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan Bindiga a Kano bayan Fara Kai Hare Hare

  • Dubun wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne ta cika a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano, sun samu nasarar cafke mutanen ne yayin wani samame a karamar hukumar Shanono
  • Kwamishinan 'yan sandan Kano ya bada tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargin mambobin wata kungiyar ƴan bindiga ne.

Rundunar 'yan sandan ta kuma karfafa matakan tsaro a wasu yankuna na jihar, musamman a karamar hukumar Makoda.

'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga a Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa, Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, an kashe miyagu kusan 100 a Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke 'yan bindiga a Kano

A cewar Ibrahim Adamu Bakori, an cafke mutanen da ake zargin ne a daren ranar Juma'a, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Ya ce jami’an rundunar daga sashen yaki da satar mutane tare da na Shanono sun gudanar da samame na musamman da misalin karfe 2:00 na daren ranar Juma’a.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri daga mazauna kauyen Farin Ruwa a karamar hukumar Shanono.

Ya bayyana cewa waɗanda aka kama ana zarginsu da haɗin gwiwa da wasu ƴan bindiga da ke kokarin shiga Kano daga wasu yankuna na jihohi makwabta.

Hakazalika yace an fara bincike domin gano cikakken tsarin kungiyar tare da kama sauran mambobinta.

"Kokari da haɗin kan al’ummar Farin Ruwa ya taimaka wajen nasarar wannan samame."

- Ibrahim Adamu Bakori

Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da kasancewa masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi da ba a saba gani ba ga hukumomin tsaro domin kare lafiyar al’umma.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Babbar jami'a a rundunar yan sanda ta rasu bayan an mata tiyata

'Yan sanda na sulhunta manoma da makiyaya

A wani labari mai nasaba da haka, kwamishinan 'yan sandan ya ce rundunar tana gudanar da taron sulhu tsakanin manoma da makiyaya a Unguwar Barebari da ke cikin karamar hukumar Makoda, domin kawo karshen rikicin da ke faruwa a yankin.

Ya ce an gudanar da taro karkashin jagorancin kwamandan yankin Dambatta, ACP Mohammed Gwarzo.

Hakazalika an yi sannan wani zama na biyu karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda a hedikwatar rundunar domin samo mafita ta dindindin.

'Yan sanda sun kama 'yan bindiga a Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook
“Rundunar ‘yan sanda ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyi, da tabbatar da cewa jihar Kano ta ci gaba da zama wajen samun kwanciyar hankali ga kowa da kowa."

- Ibrahim Adamu Bakori

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan yaki da laifuffuka a fadin jihar tare da kira ga jama’a su ci gaba da bada hadin kai da bayanan sirri don taimakawa jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An kama dalibin jami'ar IBB kan saboda gwamna a Facebook

Sojoji sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga a jihar Kebbi.

Sojojin sun hallaka 'yan bindiga guda 80 tare da kwato babura da dama a hannunsu a karamar hukumar Ngaski.

Jami'an tsaron sun samu nasarar ceto wasu mutane wadanda miyagun 'yan bindigan suka yi garkuwa da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng