Fadar Vatican da Kanta Ta Tsage Gaskiya kan Zargin Kisan Kiristoci, Ta Yi Gargadi
- Sakatare Janar na Vatican, Pietro Parolin, ya ce rikice-rikicen tsaro a Najeriya ba na addini ba ne, amma suna da tushe na zamantakewa
- Ya bayyana cewa Musulmai ma suna cikin wadanda ke fuskantar tashin hankali daga ‘yan ta’adda da ba sa bambanci wajen kai hare-hare
- Bishop John Bakeni na Maiduguri ya ce talauci, sauyin yanayi da rikicin filaye suna daga cikin dalilan tashin hankali a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rome, Italy - Sakatare Janar na fadar Vatican, Pietro Parolin, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa na kisan Kiristoci a Najeriya.
Parolin ya bayyana cewa matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta ba su samo asali daga addini ba, sai dai daga dalilan zamantakewa.

Source: Twitter
Vatican ta magantu kan zargin kisan Kiristoci
Parolin ya bayyana haka ne a birnin Rome yayin wani taro da aka shirya don gabatar da rahoton kungiyar 'Aid to the Church in Need' (ACN) kan ‘yancin addini a duniya, cewar The ICIR.
Yayin da yake mayar da martani kan rahotannin karin hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya, limamin ya ce rikicin manoma da makiyaya a Arewacin Najeriya misali ne da ke nuna cewa dalilan ba na addini ba ne.
“Wannan ba rikicin addini ba ne, ya kamata mu gane cewa Musulmai da dama ma suna zama kan gaba wajen fuskantar irin wannan tashin hankali.”
Ya ce wadannan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ba sa nuna bambanci a lokacin da suke cimma manufarsu, suna kai hare-hare kan duk wanda suka ga abokin gaba ne.

Source: Facebook
Rabaran ya fadi tushen rikici a Najeriya
A wani bangare, Bishop John Bakeni a Maiduguri ya ce tushen rikicin da ke addabar Najeriya ya kunshi abubuwa masu rikitarwa kamar talauci, sauyin yanayi da rikicin filaye.
Sai dai ya jaddada cewa akwai wasu hare-hare da suke nuna fuskar addini, inda ‘yan bindiga ke kai hari kan coci-coci da limaman Kirista ba tare da tsoro ba.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
Maganganun shugabannin Katolika sun zo ne a daidai lokacin da ake samun damuwa daga ‘yan majalisar dokoki na kasashen waje, wadanda ke bayyana abin da ke faruwa a Najeriya a matsayin “kisan gilla ga Kiristoci.”
Sai dai gwamnatin tarayya ta ƙaryata wannan ikirari, tana mai cewa ba a nufin bangare daya kadai, kamar yadda Catholic News Agency ta ruwaito.
Bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron 'Aqaba Process' da aka yi a Rome, Massad Boulos, mai ba da shawara na musamman ga tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ‘yan ta’adda suna kashe Musulmai fiye da Kiristoci a Najeriya.
Ya kara da cewa gwamnatin Amurka za ta ci gaba da hada kai da Najeriya wajen magance matsalolin tsaro gaba daya.
An gano masu yada kisan Kiristoci a Najeriya
Kun ji cewa wani bincike ya gano yadda kafafen sada zumunta suka taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ingiza ikirarin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.
Daga farko daga watan Maris 2025, an gano karuwar ambaton wannan batu mai hadari, wanda ya fara daukar hankalin duniya.
Binciken ya gano cewa daga ƙasa da sakonni 5,000 da aka wallafa a tsakanin Maris zuwa Yuli, ya karu zuwa kusan 20,000 a watan Oktobar 2025.
Asali: Legit.ng
