Kano: Hisbah Ta Dakile Shirin Auren Jinsi a Kano, an Cafke kusan Mutum 30
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta samu nasarar dakile wani shirin auren jinsi da aka yi yunkurin gudanarwa tsakanin wasu matasa
- An samu nasarar dakile shirin ne bayan samun bayanan sirri da ke tabbatar da shirye-shiryen gudanar da bikin
- Hakazalika, hukumar ta samu nasarar cafke wasu mutane cikin har da 'yan daudu da mata a yayin samamen da jami'anta suka kai a wurin bikin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta hana wani bikin auren jinsi tsakanin maza da ake zargin an shirya.
Hukumar Hisbah ta ce an kama mutum 25 da ake zargi da hannu a lamarin.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin shugaban hukumar (bangaren ayyuka na usamman), Sheikh Dr. Mujahid Aminuddeen Abubakar, ya tabbatar da hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Hisbah ta dakile auren jinsi
A cewar hukumar, an kama mutanen ne da daddare a ranar Asabar a wani dakin taro da ke kan titin Hotoro Bypass, cikin karamar hukumar Tarauni ta jihar.
Mataimakin shugaban Hisbah ya bayyana cewa aikin ya biyo bayan bayanan sirri daga wani mazaunin yankin da ya sanar da hukumar.
Ya ce bayanan sirrin sun nuna cewa wani Abubakar Idris yana shirin yin aure da wani saurayi, inda jami’an Hisbah suka yi gaggawar kai samame a wurin da aka shirya taron, kuma suka tarar da ana shagalin biki cikin duhun wuta.
“Da muka isa wurin, jami’anmu sun tarar da taron samari da ‘yan mata suna gudanar da abin da aka bayyana a matsayin bikin aure."
- Dr. Mujahid Aminuddeen Abubakar
Hisbah ta cafke wadanda ake zargi
Ya ƙara da cewa jami’an sun kama mutum 25 a wurin, ciki har da ‘yan daudu 18 da kuma mata bakwai daga yankuna daban-daban kamar Sheka, Yar Gaya, da Kofar Nasarawa.
Dr. Mujahid ya bayyana cewa dukkanin wadanda aka kama suna tsare a ofishin Hisbah, kuma za a gurfanar da su a kotun shari’a bayan an kammala bincike.

Source: Original
Ya roƙi iyaye da masu kula da yara su rika koya musu kyawawan ɗabi’u da tarbiyya, tare da kira ga jama’a su rika sanar da hukumar Hisbah ko hukumomin tsaro idan sun ga wani aiki da ya saba wa ɗabi’un al’umma.
Mataimakin shugaban ya jaddada cewa hukumar Hisbah za ta ci gaba da kokarin inganta tarbiyyar al’umma da kare martabar jihar Kano a matsayin al’umma mai bin dokokin addini da ladabi.
Hisbah ta soke shirin auren Mai Wushirya
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta soke shirin aurar da shahararrun 'yan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya da Basira 'Yar Guda.
Hukumar Hisbah ta bayyana cewa ta soke shirin auren ne bayan bincike ya nuna cewa dukkkansu ba su so, kuma tun da farko sun amince da batun auren ne domin kaucewa hukuncin kotu.
Hakazalika, hukumar ta bayyana cewa za ta maida lamarin gaban kotu domin daukar matakin shari'a na gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

